NA YI RANTSUWA DA KABARIN MAHAIFINA, MENENE MAFITA

Share:

                                ﷽


Tambaya

Assalamu alaikum warahmatullah

Allah ya karawa malan lpy dan Allah ga wata tmby daga wani dan uwa : Abokinmu ne ya rantse da kabarin iyayensa cewa baze dawo yayi aiki tare damu ba saboda wata matsala data shiga tsakani,   to yanzu kuma yana so ya dawo muma muna so, yayi rantsuwar ne cikin fushi meye hukuncin kaffararsa zeyi azumi uku ne ko me zeyi??


Amsa

Wa alaikum assalam,rantsuwa da kabarin iyaye ba ta inganta ba, duk wanda zai yi rantsuwa,ya rantse da Allah ko kuma ya yi shiru,kamar yadda ya tabbata a hadisi, rantsuwa da wanda ba Allah ba karamar shirka ce. 

Ya dawo ya cigaba da aikinsa,ba ya bukatar kaffara,ya yawaita istigfari saboda abin da ya yi zunubi ne. 

Allah ne mafi sani


DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

No comments