YA TSOTSI NONON BUDUWARSA, KOZASU IYA AURE ?

Share:
Tambaya
Assalamu alaykum. Tambaya malam
saurayi da budurwane shaidan
yashiga tsakaninsu har yakaiga
saurayin ya tsotsi qirjin budirwan
har saida ruwa ya fito. Hakan yafaru
ba so dayaba ba biyu ba amma bata
taba ganin ruwanba sai ranar. To
mallam yaya hukuncin aurensu, ya
halatta suyi auren?
Kuma minene hukuncin shan Ruwan
da yayi?
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To dan'uwa wannan abin da suka
aikata mummuna ne, Tun da Allah ya
haramta taba jikin matar da ba ka
aura ba, kuma kofa ce da za ta kai
zuwa zina, idan mutum ya tsotsi
nonan mace bayan ya girma Amma
babu ruwa a ciki, wannan ba zai
haramta musu aure ba, amma idan
akwai ruwa a ciki, to
malamai sun yi sabani akan hakan
zuwa maganganu guda biyu :
1. Ya halatta su agonce, saboda
kasancewar nonon da yake haramta
aure
shi ne wanda aka sha kafin yaro ya
cika shakaru
biyu, saboda fadin Annabi s.a.w.
“Shayarwar da
take haramtawa, ita ce wacce yaro ya
sha
saboda yunwa” , Bukhari lamba ta :
5102,
ma’ana lokacin da ba zai iya
wadatuwa ba daga
nono, saboda shi ne abincinsa, shi
kuma wannan
ya faru ne bayan mutum ya girma
don haka ba
zai yi tasiri ba wajan haramta aure,
wannan ita
ce maganar mafi yawan malamai.
2. Yana haramta aure, saboda ko da
yaushe
mutum ya sha nonon mace to ta
haramta a gare
shi, domin Annabi s.a.w. ya umarci
matar Abu-
huzaifa da ta shayar da Salim, don ta
haramta a
gare shi, kamar yadda Muslim ya
rawaito a
hadisi mai lamba ta : 2636, tare da
cewa a
lokacin Salim ya riga ya girma,
wannan sai yake
nuna cewa idan babba ya sha nono to
zai yi
tasiri wajan haramcin aure. Zancen
da ya fi karfi
shi ne nonon da mutum ya sha bayan
ya girma ba ya haramta aure a
tsakaninsa da matar da ta ba shi.
Don neman Karin
bayani duba : Bidayatul-mujtahid
2\67.
Duk wanda ya kiyaye dokokin Allah,
tabbas zai kiyaye shi, Wanda ya saba
masa zai same shi a madakata.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu zarewa

No comments