SHIN YA HALATTA NA AURI CRISTER?

Share:

Tambaya
Malam musulmi zai iya auren Ahlul kitab ta na
addininta yana musuluncinsa?
Amsa
To dan'uwa Allah madaukaki ya halatta auren
kamammu daga cikin ahlul-kitabi, wato
Yahudu ko Nasara, kamar yadda ya yi bayanin
hakan a cikin suratul Ma'ida a aya mai lamba
ta: (5), kuma an samu wasu daga cikin
sahabai, sun aure su kamar Usman dan Affan
- halifa na uku a musulunci- ya auri
Banasariya, haka Dalhatu dan Ubaidillah ya
auri Banasariya, sannan Shi ma Huzaifa
masanin sirrin Annabi ﷺ ya auri Bayahudiya,
Allah ya kara musu yarda. Duba: Ahkamu-
ahlizzimah 2\794.
Saidai malaman wannan zamanin suna cewa,
abin da ya fi shi ne rashin auren Ahlul-kitab a
halin yanzu, saboda yadda zamani ya canza,
domin da yawa idan mijinsu musulmi ya mutu
yaran suna zama cirister, kai wani wani
lokacin ko da sakinta ya yi za ta iya guduwa
da yaran, sannan zai yi wuya ka samu
kamammu wadanda ba su taba zina ba a
cikinsu.
Wasu kasashen kuma idan za ka auri cirister
daga cikinsu dole zai ka yarda da dokokin
kasarsu, a lokuta da yawa kuma za ka samu
dokokin sun sabawa ka'idojin musulunci.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

1 comment:

  1. ya halatta mutum ya karbi kudi zai siyo wani Abu sai ya nema ya rasa saiya gyara shi kuma rike kudin a matsayin ya sayo wani ya daura?

    ReplyDelete