IDAN KWARTO YA DANGANTAWA KANSA DAN ZINA ZAI IYA CIN GADONSA?

Share:

Tambaya
Asslamu alaikum. Malan don Allah amin bayani
akan dan zina, wanda an san hakikanin wanda
ya yi cikin. shin zai ci gado?, za a iya
ambatarsa da sunan wanda yayi cikin?,
Amsa
To dan'uwa wannan mas'alar ta kasu gida
biyu:
1. Maganar mafi yawan malamai ita ce: dan
zina ba'a danganta shi zuwa kwarto, don haka
ba zai ci gadonsa ba, saboda fadin Annabi ﷺ
"Da na mai shimfida ne, shi kuma kwarto ba
shi da hakki" kamar yadda Bukari ya rawaito a
hadisi mai lamba ta: 6368.
2. Idan har matar ba ta da aure kuma wanda
ya yi zinar ya danganta dan da aka samu ta
wannan hanyar zuwa gare shi, kuma ba wanda
ya ja da shi akan haka, to ya halatta a
danganta masa dan, masu wannan maganar
sun kafa hujja da cewa: hukuncin da Annabi
ﷺ ya yi na cewa: Yaro ana danganta shi ne
ga mai shimfida, yana kasancewa ne ga matar
aure, amma wacce ba ta da aure, idan ta yi
zina, kuma kwarto ya ce ya ji ya gani, za'a iya
danganta shi zuwa gare shi, Wannan shi ne
ra'ayin Urwa da Ibnu Siiriin da Ishak dan
Rahuya da Ibnul-kayyim.
Wannan yana nuna cewa duk matar da take da
miji, idan aka yi zina da ita, to za'a
dangantawa mijinta abin da aka samu, saboda
hadisin da ya gabata, amma matar da ba ta da
miji, to kwartonta zai iya danganta dan aka
samu zuwa gare shi a maganar wasu
malaman, in har ya danganta kuma, to zai
dauki dukkan hukunce-hukuncen da ake bawa
cikakken Da.
Allah ne mafi sani.
Don neman Karin bayani duba: Zadul-ma'ad
5\374.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

No comments