DAN ZINA ZAI GAJI MAHAIFIYARSA?

Share:

Tambaya
Assalamu alaykum. Malam don Allah Malam
innada tanbaya, Malam mace ce tayi cikin
batare da aure ba, ta haihu kuma tana da kudi
sai Allah yamata rasuwa toh malam yaron
zaici gadonta.
Amsa
Wa'alaikum assalam, idan mace ta yi cikin
shege kuma ta haifi Da, daga baya ta mutu
Dan zinar da ta haifa zai gaje ta, saboda Allah
madaukakin sarki a cikin suratun Nisa'i aya ta:
10 ya yi wasiyya a bawa 'ya'yaye gado, Dan
zina kuma yana cikin jerin 'ya'yayen
mahaifiyarsa, wannan yasa zai gaje ta.
Dan zina ba ya gadon mahaifinsa a wajan mafi
yawancin malamai, ko da kuwa ya yarda dansa
ne.
Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

No comments