WASIYYOYI GA MAHADDATA QUR'ANI 009

Share:

WASIYYOYI GA MAHADDATA QUR'ANI 009
Sako Daga
Sheikh Mustapha Baba Ilelah
Chairman Bauchi Qur'anic Recitation competition
1- Menene Ayah,Me ake nufi da Ayah,Qur'ani ayoyi Nawa ta kansa.
2-Kaifiyyar saukar wahayi
3-Farkon abin da ya fara sauka da ayar Karshe
4- Surah makkah da Madinah
MENENE AYAH,ME AKE NUFI DA AYAH,QUR'ANI AYOYI NAWA TA KUSA
Ma'anar ayar Qur'ani itace wata sashi na harufofi,ko kalmomi wanda tana da farko da Karshe.
Kuma an ciro shi daga surah Zuwa surah na kur'ani.
Sanin farko da karshen aya tana komawa ga girman Haddar Qur'ani da sahabban annabi saw suke da ita,da girmar sha'anin su wajen Jeranta ayoyin Qur'ani.
Sanin farko da karshen ayoyin Qur'ani ta kasance daga dacewa daga annabi saw ba wai ra' ayi bane,saboda jibril AS yana saukar da ayoyin Qur'ani ga annabi saw ya kuma nusar dashi Inda ya kamata a sanya wannan ayoyi sannan ya umurci sahabbai da a sanya ta a lambar aya ta......
ADADINI AYOYIN QUR'ANI
Malaman Ulumul Qur'ani sun yi sabani akan adadin ayoyin Qur'ani saboda banbancin riwaya kamar haka:-
1-6000
2-6024
3-6224
4-6219
5-6225
6-6226
Adadin Kamomin Qur'ani 7737,Adadin Harufofin Qur'ani 321.
*MENENE SURAH*
Surar Qur'ani wata yan ki ce ta Qur'ani tana da farko da Karshe.
Malamai sun karkasa surah zuwa kashi hudu kamar haka:-
1- ﺍﻟﺴﺒﻊ ﺍﻟﻄﻮﺍﻝ
Bakwai masu tsayi sune:-
Bakarah,Ali-imran,Nisa'I,Ma'idah,An'am,A'araf
,Taubah.
2- ﺍﻟﺴﻮﺭ ﺍﻟﻤﺌﻮﻥ
Itace surar da ayar ta ta karu akan dari kamar suratul Nahli,Suratu yusuf.
3- ﺍﻟﺴﻮﺭ ﺍﻟﺜﻤﺎﻧﻲ
Itace surar Mai dauke da ayoyi dari biyu,ko itace Mai dauke da mafi karanci aya dari,kamar suratul Hajj,Suratul Furkan.
ADADIN SURORIN QUR'ANI
Surori guda dari da goma sha hudu 114
- Surar Makkah 82
- Surar Madinah 20
Akwai surori guda 12 wanda galibinsu na makkah ne,a ciki akwai wanda da yawansu na madinah ne.
*MENENE SURAR MAKKAH DA MADINAH DA ALAMOMINSU*
- Surar Makkah itace wanda aka saukar kafin hijira,ko da a garin madinah ta sauka.
- Surar Madinah itace wanda ta sauka bayan hijira,ko da saukar ba'a garin Madinah bane.
Wasu maluma su kace Makkah itace wanda aka saukar a makkah,Madinah kuma wanda aka saukar a Madinah.
ALAMOMIN GANE SURAR MAKKAH DA TA MADINAH
MAKKAH
1- Samun lafaci ﻛﻼ a wajen talayi Fa uku.
2-Sura Mai sujuda a cikin ta.
3- Farawa da kuramen Baki (ﺍﻟﻤﺺ،ﺍﻟﻢ ) Banda bakara da Ali-imran
4-Samun kissoshi da labarai.
5-farawa da yaku mutane
MADINAH
1-Hukunce-Hukunce na shari'ar musulunci
2-Jihadi da hukunce-Hukuncin ta
3-Bada labarin munafikai
4-Bayanin Halal da haram
5- farawa da yaku wanda ku kayi imani.
Akwai ayoyin da aka saukar dasu kamar haka :-
1- ﺍﻟﺤﻀﺮﻱ ﻭﺍﻟﺴﻔﺮﻱ
-2 ﺍﻟﻴﻠﻲ ﻭﺍﻟﻨﻬﺎﺭ
-3 ﺍﻟﺼﻴﻔﻲ ﻭﺍﻟﺸﺘﺎﺋﻲ
-4 ﺍﻟﻔﺮﺍﺷﻲ ﻭﺍﻟﻘﻮﻣﻲ
FARKON AYAR DA TA FARA SAUKA DA KARSHEN SAUKA
Farkon ayar da ta fara sauka na Qur'ani suratul Alak.
ﺍﻗﺮﺃ ﺑﺴﻢ ﺭﺑﻚ ﺍﻟﺬﻱ ﺧﻠﻖ، .. ﺇﻟﻲ ﻗﻮﻟﻪ ﻋﻠﻢ ﺍﻹﻧﺴﺎﻥ ﻣﺎﻟﻢ ﻳﻌﻠﻢ
Ayar karshen sauka itace suratul ma'idah.
ﻳﺴﺘﻔﺘﻮﻧﻚ ﻗﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﺄﺗﻴﻜﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﻜﻠﻠﺔ .
Wasu suka ce itace a suratul Bakarah
ﻭﺍﺗﻘﻮﺍ ﻳﻮﻣﺎ ﺗﺮﺟﻌﻮﻥ ﻓﻴﻪ ﺇﻟﻲ ﺍﻟﻠﻪ .
Mu Hadu a kashi na 10
Fassar wasiyyoyi
Abdurrahman Adamu Aliyu Jahun

No comments