WASIYYOYI GA MAHADDATA QUR'ANI 008

Share:

WASIYYOYI GA MAHADDATA QUR'ANI 008
      Sako Daga
     Sheikh Mustapha Baba Ilelah
Chairman Bauchi Qur'anic Recitation competition

1-Ma'anar Qur'ani
2-Sunayen Qur'ani da Siffofin ta
3-Saukar Qur'ani
4-Fa'idojin saukar Qur'ani lokaci Bayan lokaci
5-Banbancin Qur'ani da Hadisul Qudsi
6-Banbancin Qur'ani da Hadisin Annabi saw.

MA'ANAR QUR'ANI
Maganar Allah Mai mu' jiza,wanda aka saukar wa annabi Muhammad saw,ta hanyar mala'ika jibril AS,wanda aka rubuta a mushafi wanda ake bautar Allah da karanta shi,wanda ya fara daga suratul fatiha Zuwa suratul Nas.

SUNAYEN QUR'ANI DA SIFFOFINTA
Qur'ani tana da Sunaye masu yawa daga cikin su akwai:-
1-الفرقان                                                                           Mai rabe tsakanin Gaskiya da kar     
2-الكتاب                                                An kiraka littafi ne saboda ta kunshi ilmomi,labari
3-التنزيل
4-الذكر
Wannan sune Sunaye masu shahara na Qur'ani sai dai wasu Malamai sun kara,Amma ba Sunaye bane siffofi.
shiga ka karanta

SIFFOFIN AUR'ANI
Akwai siffofi masu yawa a Qur'ani Amma daga cikin su kamar:-
1-الرحمة :Jinkayi
2-الشفاء : Waraka daga cutuka
3- الحبل :Igiya Mai karfi
4-الفصل : Rabewa
5- المجيد : Mai girma
6-بشير ونذير : Mai Bushara da gargadi
7-النور : Haske
8-أحسن الحديث : Kyakyawar Zance
9-العزيز : Mai girma
10-البشري : Bushara
  SAUKAR QUR'ANI
Qur'ani ta sauka a matakaiya uku (3)

1- Lauhul Mahfuzi(اللوح المحفوظ)
2- Baitul Izzah Zuwa sama ta duniya(بيت العزة إلي مساء الدنيا )
3-Sauka ta hanyar mala'ika jibril AS a zuciyar annabi saw.

LOKUTAN SAUKAR DA QUR'ANI
An fara saukar da Qur'ani da wahayi wa annabi saw a  17-Ramadan-13AH,Annabi saw yana Shekara ta 41 a rayuwar sa,A cigaba da saukar wahayi har shekara 23 har ya Hadu da ubangijin sa a shekara ta 13-Rabiul Auwal-23AH wanda ya yi dai dai da 8-Yuni-633CE yana da shekara 63.

FA'IDOJIN SAUKAR DA QUR'ANI LOKACI BAYAN LOKACI
Akwai hikimomi masu yawa da Allah SWT ya ke saukar da Qur'ani lokaci Bayan lokaci kamar haka:-
1-Tabbatar da ita a zuciyar annabi saw
2-Bin Matakaiyar tarbiyar al'umma
3- Saukake Haddar ta da Fahimta
4-Amsa tambayoyin masu tambaya akan wasu waki'a
5- Shiryarwa daga madogarar Qur'ani itace kadaituwar Allah.

BANBANCIN HADISIN QUDSI DA QUR'ANI
- QUR'ANI
1-Ana bauta da karanta shi
2- Tana da mu'ujizozi ta gagara bada
3-Bashi halarta riwayarta da ma'Ana
4- An haramta ma wanda bashi da tsarki rike ta
5- Mutawatiri har Zuwa ga annabi saw
6-Wanda ya musanta aya daga cikin ta Ya kafirta

HADISUL QUDSI
1-Ba'a bauta da karanta shi
2- Ba'a nufin mu' ujiza da it a
3- Ta halarta riwayarta da ma' ana a wajen dayawa a maluman Hadisi
4-Ba'a haramtawa mai hadasi daukarta
5-Ba'a kafirta wanda ya musanta shi
6- Allah bai dauki alkawalin kareta ba.

BANBANCIN QUR'ANI DA HADISIN ANNABI SAW
- Hadisi shine abin da ya samu madogara daga annabi saw wajen zance da Furuci,ko abinda ya tabbatar ko sifanta.
- Kur'ani itace littafin da Allah ya saukar wa annabi saw.


           Mu Hadu a kashi 009

           Fassar wasiyyoyi
     Abdurrahman Adamu Aliyu Jahun
   

No comments