WASIYYOYI GA MAHADDATA QUR'ANI 007

Share:

WASIYYOYI GA MAHADDATA QUR'ANI 007
      Sako Daga
     Sheikh Mustapha Baba Ilelah
Chairman Bauchi Qur'anic Recitation competition

1-Kyawawan Dabi'u ga Mahaddata Qur'ani
2-Miyagun Dabi'un Mahaddata Qur'ani
3-Mahaddata Qur'ani ku zauna da limaman Unguwar ku lafiya


KYAWAWAN DABI'U GA MAHADDATA QUR'ANI
Allah madaukakin sarki ya kawo kyawawan dabi'u a Qur'ani da ya kamata dukkan ma'abucin Qur'ani ya siffantu dasu kamar haka :-

-Kyakyawar Niyya
Annabi saw yace Lallai dukkan aiki na tare da Niyya,kowani Mutum yana tare da abin da ya niyyata.
Imamul Nawawi yace farkon abinda mahaddaci zai Kiyaye kyautata niyyar sa,yin aiki saboda da Allah Ta'ala.
Ibn Abbas RA yace ana kiyaye Mutum ne gwargwadon abin da ya niyyata.

-Kauda kai daga abin duniya
Yana cikin abin Da mahaddata zasu Kiyaye na dabi'u gujewa duniya ta dukiya,ko shugabanci,ko yabon mutane,ko mutane su karkata Zuwa wajensa.
أولاً: الصدق
1-Gaskiya
 قال الله سبحانه وتعالى في آياته الكريمة (يا أيُّها الّذين آمنوا اتقوا الله وكونوا مع الصّادقين). 
Ya ku wanda ku kayi imani ku ji tsoron Allah ku kasance tare da masu gaskiya.
ثانيّاً: الأمانة
2-Amana
قال الله سبحانه وتعالى في آياتهِ الكريمة (يا أيُّها الّذين آمنوا لا تخونوا الله والرّسول وتخُونوا أمانتكُم وأنتم تعلمون).
Ya ku wanda ku kayi imani kar ku ha'inci Allah ku ha'inci amanoninku Alhali kuna masa na.
ثالثاً: التواضع
3-kankan da kai tawalu'u
ُ قال اللهُ سبحانهُ وتعالى في آياتهِ الكريمة ( واخفض جناحكَ لمن اتبعك من المؤمنين).
Saboda ka zamto musulmi na kwarai wajibi ne ka zamto Mai tawalu'u a tsakanin y'an uwanka musulmi,kar ka zamto Mai girman kai ga mutane Dan Allah ya sanya ka daga cikin mahaddata Qur'ani,ka zamto Mai tawali'u.
رابعاً: العفو
4-Afuwa da yawaita
قال الله سبحانه وتعالى في آياتهِ الكريمة (فاعفُ عنهم واصفح إنّ اللهُ يُحب المُحسنين).
Ku yi afuwa da rangwame lallai Allah yana son masu kyautatawa.
خامساً: الصبر
5-Hakuri
 قال في آياتهِ الكريمة (يا أيُّها الّذين آمنوا اصبروا وصابروا).
Ya ku wanda ku kayi imani kayi hakuri ku doge a lokacin yalwata da lokacin fitina.

سادسا:الرحمة بالوالدين  قال في  آياتهِ الكريمة (واخفض لهما جناح الذل من الرحمة وقل ربي ارحمهما كما ربّياني صغيرا).
6- kasaukar da fifiken ga iyayenka na Jin kayinsu,kace Allah ya jikayinsu kamar yadda suna raine ni ina karami

سابعاً: الشكر
7-Godiya ga Allah akan ni'ima
وقال الله تعالى في آياته الكريمة (إذ تأذّن ربُكُم لئِن شكرتم لأزيدنّكُم ولئِن كفرتُم إنّ عذابي لشديدٌ).
Ubangijinku ya yi yekuwa cewa idan ku ka gode zai kara musu,Amma idan kuka kafirce Lallai azabarsa Mai tsanani ne.
Dasauransu wanda bamu ambata su ba.

MIYAGUN DABI'UN MAHADDATA QUR 'ANI
1- Chin Amana
2-Rashin Gaskiya
3-Raina mutane
4-Neman Matan Banza
5-Girman kai da ganin ya fi kowa
6-Raina Iyaye
7-Raina na gaba dashi
8-Rashin kunyar idon mutane
Dasaurar dabi'u miyagu da mahaddata Qur'ani ke dashi,muna fatar Allah ya stare mu daga wannan dabi'u.

MAHADDATA QUR'ANI KU ZAUNA DA LIMAMAN KU LAFIYA

Yana daga cikin matsaloli da a Yau a ke samu tsakanin limamai dattawa da matasa shine,su dattawa suna karanta Qur'ani da kuskure kuma Sun ki su koyi karatu Mai Tajwidi,shi kuma matashi yana Dan Bana B akwai a Haddar Qur'ani saboda ganin kuskuren limamin sa a Karatun sallah sai ya fara shirin yin Justin mulkin limanci ga wannan limami sai a fara samu takaddama tsakanin Juna.
Dan haka shi liman ya gyara Karatun sa Dan rage fitina da Matasa y'an Bana
 Bakwai.
Shi kuma mahaddaci ya yi hakuri a bi matsalolin a hankali har a shawo kansu ba tare da hatsaniya ba.


Mu Hadu a kashi na 008

           Fassar wasiyyoyi
     Abdurrahman Adamu Aliyu Jahun
   

No comments