WASIYYOYI GA MAHADDATA QUR'ANI 006

Share:
WASIYYOYI GA MAHADDATA QUR'ANI 006
      Sako Daga
     Sheikh Mustapha Baba Ilelah
Chairman Bauchi Qur'anic Recitation competition

1-Wajibi ne a karanta Qur'ani da Tajwidi
2-Hukuncin karanta Qur'ani ba Tajwidi
3- Koyan Karatun Qur'ani daga bakin Malami

WAJIBI NE KARANTA QUR'ANI DA TAJWIDI
التجويد في اللغة:- التحسين أو الإتيان بالجيد.

Kalmar Tajwidi a yaren larabci Shine kyautatawa ko Zuwa da Abu Mai kyau.
التجويد في الاصطلاح:-هو إخراج كل حرف من محرجه مع إعطاء كل حرف حق ومستحقه من الصفات والمدود وغير ذلك.
Tajwidi a wajen maluman bangaren shine fitar Da kowani harafi daga mafitarsa tare da bada kowani harafi hakkinsa da abinda ya cancance shi na siffofi da maddodi.

Dalili a Littafin Allah da Hadisan annabi saw
- قوله تعالي:-ورتل القران ترتيلا
قال العلماء أي وجود القران تجويدا،والأمر هنا الوجوب
Allah yace:-Ku rera Qur'ani rerawa,Malamai suka ce wato ku kyautata Qur'ani kyautatawa,Umurni a wannan aya tana wajabtawa ne.
قوله تعالي:الذين ءاتيناهم الكتاب يتلونه حق تلاوته أولئك يؤمنون به.
قال العلماء:-الذين ءاتيناهم الكتاب يجودونه حق تجويده أولئك يؤمنون به.
Allah ya ce:-Wanda aka basu littafi suna karanta shi kuma su suka yi imani dashi.
Malamai suka ce:-Wanda aka basu littafi suna kyautata shi hakikanin kyautata shi kuma su suka yi imani dashi.

Dalillin a Sunnar annabi saw
Annabi saw yace hadisin Abi hurairah RA yace:-Allah bai yi izini ma wani ba,fiye da izini da ya yi wa annabinsa wajen kyautata sauti.
Sheikh Ibnil Jazari RH yace:-wannan sunnar Allah ce wajen duk wanda zai ka karanta Qur'ani da Tajwidi,kamar yadda aka saukar wajen jin dadin saurararsa da tilawarsa da samun tsoron Allah a zukata lokacin karanta shi.

Malamai sun yi Ijma'i akan cewa ba'a samu daga annabi saw ko daya daga cikin sahabban annabi saw ko Tabi'ai ko shuwagabannin kira'a cewa sun karanta Qur'ani ba tare da Tajwidi ba,kuma sun yi Ijma'in akan Barin karantawa ba tare da Tajwidi ba.
Tajwidi ya kasu kashi biyu
1-Tajwidi na Ilmi
2-Tajwidi na aiki
1-Tajwidi na Ilmi itace fitar da kowani harafi hakkinsa da abinda ya cancance shi,na ka'idojin Tajwidi da sauransu.
Wannan mataki na Ilmi itace ake cema farillar da wani ka dauke ma wani (فرض كفاية)in wasu sun tsaya akai to sun wadatar wa saura.
2-Tajwidi na aiki itace Tajwidi na duk wani musulmi da zai karanta Qur'ani sai ya bi ka'idojin Tajwidi.

HUKUNCIN KARATUN QUR'ANI BA TAJWIDI
Sheikh Mahmoud Khalil Husary yace a Littafin sa(احكام قراءة القران الكريم )
Kamar yadda ya gabata Tajwidi ya kasu kashi biyu
- Ilmi
- Aiki
Bangaren ilmi Hukuncin sa tana da Alaka da dukkan musulmi kuma mustahabbi ne ba wajibi ba,saboda ingancin karatu ba shi tsayuwa kawai akan Sanin hukunce-hukunce ita ma kamar saurar ilmukan shari'a ne wanda ibadar bata yiwuwa sai da sanin sa.
  Nasabar ilimin Tajwidi a ilmance farilla ce da wani ke dauke ma wani.
Kuma bangaren aiki hukuncinsa wajibi ga dukkan wanda zai karanta Qur'ani namiji ne ko mace saboda tabbacin haka a Qur'ani da Hadisi.

ما حكم قراءة القرآن بدون تجويد ؟
رقم الفتوى : 1496 الأربعاء 6 شوال 1439 - 20 يونيو 2018 1914 عطية صقر

قال علماء التجويد: تجويد القرآن الكريم واجب وجوباً شرعياً يثاب القارئ على فعله ويعاقب على تركه، وهو فرض عين على من يُريد قراءة القرآن؛ لأنَّه نزل على نبينا صلى الله عليه وسلم مجوَّداً، ووصل إلينا كذلك بالتواتر، وقد أخرج ابن خزيمة في
صحيحه عن زيد بن ثابت رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: (إنَّ الله يحبُّ أن يُقرأ القرآنُ كما أنزل).

وقال الإمام الغزالي في كتابه (الإحياء): تلاوة القرآن حقَّ تلاوته هو أن يشترك فيه اللسان والعقل والقلب، فحظ اللسان تصحيح الحروف بالترتيل، وحظ العقل تفسير المعاني، وحظ القلب الاتعاظ والتأثر.وقال ابن الجزري رحمه الله تعالى:

والأخذ بالتجويد حتم لازم=من لم يجود القرآن آثم
لأنه به الإلهُ أنزلا = وهكذا منه إليه وصلا

قال صاحب النشر في تفسير ما قاله الإمام علي رضي الله عنه في معنى الترتيل: التجويد هو حلية القراءة، ويكون بإعطاء كل حرف من حروف الهجاء حقَّه ومُستحقَّه، أي أنه يجب أن تكون حروفه مرتبة، ويردَّ كل حرف إلى مخرجه وأصله، وبلطف النطق على كمال هيئته من غير إسراف ولا تعسف، ولا إفراط ولا تكلف، والوقف هو قطع الصوت على آخر كلمة زمناً يتنفَّس فيه القارئ. اهـ.
المصدر: مجلة الوعي الإسلامي، السنة الثانية عشرة، رمضان 1396 - العدد 141

DOLENE KA KOYI QUR'ANI DAGA BAKIN MALAMAI
Sheikh Mahmoud Khalil Husary yace a Littafin sa(أحكام قراءة القران الكريم)17
Malamai suka ce ba'a Koyar Qur'ani sai ta Hanyoyi kamar haka:-
1- Dalibi ya saurara daga lafazin Sheikh ya karanta a gaban dalibai suna saurara itace hanyar magabata.
2-Dalibi ya karanta a gaban sheikh yana saurararsa itace hanyar wanda suka zo a baya.
Amma abinda ya fi falala a Hada dukkan wannan tsari biyu.

Mu Hadu a kashi na 007


           Fassar wasiyyoyi
     Abdurrahman Adamu Aliyu Jahun
   

No comments