WASIYYOYI GA MAHADDATA QUR'ANI 005

Share:

WASIYYOYI GA MAHADDATA QUR'ANI 005
      Sako Daga
     Sheikh Mustapha Baba Ilelah
Chairman Bauchi Qur'anic Recitation competition

1-Tsarin muraji'ar Qur'ani
2-Halayen magabata wajen muraji'ar Qur'ani
3-Hukuncin Karatun Qur'ani kasa da kwana uku
4-Ladubbar saukar Karatun Qur'ani da addu'oi

TSARIN MURAJI'AR QUR'ANI
Lallai muraji'a itace jigon hadda saboda a yau da yawa daga cikin mahaddata Qur'ani su mance abinda suka Haddace.
- المراجعة الفردية
Muraji'ar da mahaddaci zai yi shi kadai.
Wannan muraji'a kuwa itace raba Qur'anin Zuwa izu-izu ko sura-sura gwargwadon dawainiyar shi mahaddacin tare da ware wasu wuridi na muraji'ar da zai dinga yi kullum,wanda ya iyakance su wa kansa.
1-التدسيس
Attadsis shine mahaddaci ya dinga karanta duk izu biyar 5  a kullum wanda zai sauke a cikin sati daya.
2-التسبيع
Shine mahaddaci ya dinga sauke  Qur'ani a cikin sati daya kamar yadda sahabbai da tabi'ai ke aikatawa.
3-  الختم في عشرة ايام
Sauke Qur'ani a kwana goma a kullum mahaddaci zai dinga karanta izu uku 3.
4-الختم في خمسة عشر
Sauke Qur'ani a kwana goma sha biyar 15 kullum mahaddaci zai dinga karanta izu biyu.
5-الختم في شهر
- Sauke Qur'ani a wata guda a kullum mahaddaci zai dinga karanta izu biyu.
6-الختم كل أربعين يوما
Sauke Qur'ani a kwana arba'in a kullum mahaddaci zai dinga karanta ayoyi 155 ko 1557.

HALAYEN MAGABATA WAJEN MURAJI'AR QUR'ANI
An samu sabanin al'ad in magabata wajen muraji'arsu,Amma da yawa daga cikin su suna saukewa a cikin sati daya kamar yadda Imamul Nawawi da Imamul suyudi suka hakaito.
Saboda dalilinsu abinda ya tabbata na Hadisi annabi saw yace:-A hadisin Abdullahi bn Amru bn As R.A ku karanta Qur'ani cikin wata daya,sai yace lallai ina Jin karfi zan yi kasa da haka,sai yace ku karanta a kwana ashirin,sai yace lallai ina jin karfi zan yi kasa da haka,sai annabi saw yace:-ku karanta a kwana goma,sai yace lallai ina jin karfi,sai yace ku karanta a kwana Bakwai kar ku kara akan haka. (Bukhari 4767,muslim 1159)

Annabi saw yace:-Ba zai fahimce shi ba wanda ya karanta kasa da kwana uku. (Abu dawoud 1390,Tirmizi 2949).
Imamul Nawawi yace an Nakalto daga Zarkashi,Ibn Hajar,Suyudi cewa sahabbai da suke saukewa a cikin sati daya suna da yawa.

Imam ibn kudamah yace an so Mutum ya sauke a cikin sati daya saboda kowace sati kana da sauka daya.

Abdullah Dan Imamu Ahmad bn hambal yace Mahaifina yana saukewa a cikin sati daya.
Yace Mahaifina yana saukewa juma'a Zuwa juma'a,saboda hadisin Abdullahi bn Amru bn As.

Imamul suyudi yace:-yana biyowa wanda ya sauke a kwana takwas,wannan kwana goma sannan wata daya,sai wata biyu.
Ya kawo Hadisi cewa Sahabbai masu karfi da juriya suna karanta Qur'ani su sauke a kwana 7,wasu a wata 1,wasu a wata biyu 2,wasu kuma fiye da haka.

HUKUNCIN KARATUN QUR'ANI KASA DA KWANA UKU
Malamai sun yi sabani akan sauke Kur'ani kasa da kwana uku kamar haka :-
1-Ibn Hajar ya kawo Hadisi daga sa'I'd bn mansur da isnadi ingattaciya daga Abdullah bn mas'ud RA yace ku karanta Qur'ani a kwana Bakwai kar ku karanta kasa da kwana uku.
2-Abu Ubaid yace daga Aishatu RA tace annabi saw baya sauke kur'ani a kasa da kwana uku.
3-Wasu Malamai kamar yadda Imamul Nawawi ya kawo su kace hanin akan sauka kasa da kwana uku ba akan haramun bane,kamar yadda lamarin ba akan wajibci bane.
4-Wasu sashin Malamai na zahiriyya sun tafi akan haramun ne karantawa kasa da kwana uku.
5-Imamul Nawawi yace wasu Malamai sun tafi akan cewa ba'a kaddarata akan haka ba,Amma an yi ne gwargwadon dawainiya da nishadi, Don haka tana canzawa gwargwadon hali da lokaci.(Fathul bari 9/96)
6-Ibn mas'ud RA yace :-Wanda ya karanta kasa da kwana uku ya zamto kamar waka ce ba zai fahimce ta ba.

HUKUNCIN BIKIN  SAUKAR KARATUN QUR'ANI DA ADDU'OI
Malamai suka ce babu laifi Idan aka sauke Karatun Qur'ani a Tara mutane a gabatar da addu'oi a ci Mai kyau a sha Mai kyau kamar yadda aka samu magabata na kwarai sun aikata haka ga kadan daga cikin zantukarsu:-

1- An so yin addu'a lokacin sauke Qur'ani.
Magabata na kwarai sun kasance suna kwadaituwa hakikanin kwadaituwa akan yin addu'a lokacin sauke Qur'ani,har sun kasance suna Tara iyalansu da masoyansu wajen saukar karatun Qur'ani saboda rahama dake sauka a wajen sun kafa hujja da nassosi kamar haka:-
2- Abdullah bn mas'ud RA yace:-Duk wanda ga kammala Saukar Qur'ani to yana da addu'a karbabbiya a wajen Allah,shi ya sa in ya sauke ya akan Tara iyalansa ya yi addu'a suna cewa Amin.
3- Anas bn Malik RA ya kasance idan ya sauke Qur'ani ya kzn Tara iyalansa da y'ay'ansa ya yi musu addu'a.

Mu Hadu a kashi na shida 006

           Fassar wasiyyoyi
     Abdurrahman Adamu Aliyu Jahun
   

No comments