WASIYYOYI GA MAHADDATA QUR'ANI 004

Share:
WASIYYOYI GA MAHADDATA QUR'ANI 004
      Sako Daga
     Sheikh Mustapha Baba Ilelah
Chairman Bauchi Qur'anic Recitation competition

1-Hanyoyin saukake Haddar Qur'ani
2-Falalar Haddar Qur'ani
3-Muraji'ar Qur'ani
4-kwanakin sauke Qur'ani
5-Ladubbar Karatun Qur'ani

HANYOYIN SAUKAKE HADDAR QUR'ANI
- kyakyawar Niyya
- Addu'a akan saukin Haddar
- Istigfari da barin sabon Allah
- Hakuri da dagewa
- Ware lokaci ta musamman Dan Haddah
- Rage shagullar duniya
- Jeranta wuridi na Haddar da zaka haddace a wuni
- Sahibantar Ma' abuta Qur'ani masu hazaka
- yawaita Karatun Qur'ani a Lokuta masu falala
- Yin kokarin karanta abinda ka haddace a sallah farilla da nafila
- Muraji'ar abinda ka haddace
- Lazimtar masallaci da majalisin ilmi
- Yin aiki da abinda ka haddace
- Lazimtar Ladubbar Ma'abuta Qur'ani
- Kiyaye alwala a tare da kai a duk lokaci
- Koyar  da mutane abinda ka haddace
- Kiyaye lokaci da muhimmancin sa
- Sanin Tarihin mahaddata Qur'ani
- Yin karatu da Qur'ani da ya
- Sallar dare(kiyamul laili)da abinda ka haddace
- Kiyaye ayoyi masu kama da Jun a
- Sauraran Malamai makaranta Qur'ani na Duniya
1-Sheikh Mahmoud Khalil Husary
2- Sheikh Muhammad Siddikul minshawy
3- Sheikh Abdulbasid Abdulsamad

FALALAR HADDAR QUR'ANI
Fa'idojin suna da yawa a takaice sune:-
- Rabauta da Gidaje guda biyu duniya da lahira
- Mahaddata sune a ka basu ilmi
- Haddar Qur'ani sababi ce ta tsira
- Shi ake fara gabatarwa a labari
- Sune a gaba a duniya da lahira
- Sune limaman masallatai
- Sune a ke sanya komitin shut a
- Daukakuwar matsayi a Alanna
- Akan aura masa Mata sadakin ta Ya Koyar da ita Qur'ani
- Mutum bashi zamowa Malami sai ya haddace Qur'ani
- Sune Ahlul Allahi
- Haddar Qur'ani na sanya ka abota da mutanen Kirk

MURAJI'AR QUR'ANI
هجر القرأن
Kauracewa Qur'ani wajen karanta shi da aiki dashi
1-ترك تلاوة القرآن
Manta Haddar Qur'ani Bayan haddace shi.
2-الأعراض عن القران واللغو فيه
Kauda da kai ga Qur'ani da wargi ga littafin
3- القول فيه بغير الحق وهذا صنيع الكفار
Furuci akan sa ba tare da gaskiya ba,wannan aiki ne na kafirai
4- ترك العمل بالقرآن
Barin yin aiki da Qur'ani

Ana so mahaddata Qur'ani su dawwama wajen karanta abin da haddace,Amma ka dauki abin da zaka iya dawwama kana yi.
Kamar yadda annabi saw yace a yi riko da wannan littafi kuma ya yi misalin Rakumi da akalarta,in kayi riko da ita ta tsaya in kayi sakaci ta tafi.

KWANAKIN SAUKE QUR'ANI
Annabi saw yace ba zai fahimci Qur'ani ba wanda ya sauke kasa da kwana uku.
Saboda haka Malamai sun yi bayani cewa haramun ne saukewa kasa da kwana uku,wato sai dai kayi kullum izu 20,20,20 sai ya zamto izu 60.

LADUBBAR KARATUN QUR'ANI
1-Ladubbar zukata
-yawaita Karatun Qur'ani
- An so ka zamto cikin alwala
- Karatu a waje mai tsafta da tsarki
- Fiskantar Alkibla
- Korar shaidan lokacin fara karatu
- Yin bismillah a farkon kowace surah Banda suratul taubah.
- Jeranta Karatun Qur'ani
- In an maka sallama kana karatu ba laifi ka katse ka amsa
- Yin sujjada wajen sujjada goma sha giyar
- Karatu da Qur'ani yafi yi a haddace
- Kyautata sauti da rerawa
- Yin kuka saboda tadaburi   


Mu Hadu a kashi na 005 insha Allah.

           Fassar wasiyyoyi
     Abdurrahman Adamu Aliyu Jahun
 

No comments