WASIYYOYI GA MAHADDATA QUR'ANI 003

Share:
WASIYYOYI GA MAHADDATA QUR'ANI 003
      Sako Daga
     Sheikh Mustapha Baba Ilelah
Chairman Bauchi Qur'anic Recitation competition

1- Hanyoyin shigar da Haddar Qur'ani
2- Lokuta masu falala wajen shigar da Haddar Qur'ani
3- Haddar Qur'ani itace ilmi na farko
4- Magabata suna yara suka haddace Qur'ani


HANYOYIN SHIGAR DA HADDAR QUR'ANI
Bayan ka saurari abin da ka ke son Haddacewa daga cikin maluman Qur'ani a cikin kaset ko radio,sai ka karanta a wajen Malami,sai ka karanta kai ka dai a cikin Qur'ani sai ka Duba da ya gada cikin wannan hayoyi kamar haka:-
1-طريق حفاظ التسلسلي
Shine mafi kyawun tsarin Haddar Qur'ani wato ka yi ta karantawa da maimaita aya 01,sai ka haddace shi sai ka tafi aya ta 02 ka haddace,sai ka Hada aya ta 01 da aya ta 02 biyu ka sa ke karantawa har Zuwa karshen shafin.
2-طريق حفاظ الجمعي
Shine karanta dukkan shafin gaba daya sai ka haddace shi,sai ka dawo ka dauki ayoyi kamar 10-20 goma Zuwa ashirin a shafin ka yi ta maimai ta Su ta musamman.
3-طريق حفظ المقسم
Shine hanyar Haddar Qur'ani tsaka tsakiya tsakanin na farko da na biyu.
Bayan ka haddace da Matakin farko sai ka sanya tsarin mataki na biyu.

2- LOKUTA MASU FALALA WAJEN SHIGAR DA HADDAR QUR'ANI
Wannan Abu ne da ya sha banban gwargwadon dawaniyar dalibi,wani shi me Duba wa kansa lokaci ne Mai tsaida da falala,ko Bayan sallar asubahi ko Bayan sallar isha'i ko Bayan Azahar ko cikin dare.

Lokaci mafi tsada da dacewa shine Bayan sallar asubahi da tsakanin magriba Zuwa isha'i sai cikin dare daga karfe daya 01 Zuwa Asubahi.
Amma ba'a son shigar da Haddar Qur'ani lokacin da rana tayi zafi kamar daga karfe 12-02 sha biyu Zuwa karfe biyu.

3- HADDAR QUR'ANI ITACE ILMI NA FARKO
Magabata da yawa suna muhimmanta Haddar Qur'ani a Matakin farko kafin kowani ilmi ta shari'a.
Malamai suka ce ilimin farko shine Haddar Qur'ani da fahimtar sa,duk abinda zai taimaka maka wajen Newman ilmi to wajibi ne nemar sa,kuma ga duk wanda ke so ya zamto Malami to ya fara da Haddar Qur'ani.

Shi ya sa magabata da yawa suke korar dalibi daga majlisinsu in ya zo daukar karatu akan sai ya fara da Haddar Qur'ani.

MAGABATA SUNA YARA SUKA HADDACE QUR'ANI

1-Imamul Dabari Mai Tafsiri ya haddace Qur'ani yana Dan shekara akwai,ya fara Jan sallah yana Dan shekara takwas, ya fara rubuta Hadisai yana Dan shekara Tara.
2- Alhafizul Iraqi malamin Hadisi a kasar masar ya haddace Qur'ani yana Dan shekara takwas.
3- Sufyan ibn uyainah ya haddace Qur'ani yana Dan shekara goma sha hudu
4- Hafsat binti Sirin ta haddace Qur'ani tana y'ar shekara goma sha biyu.
5- Muhammad Amin Shankidi mai tafsiri ya haddace Qur'ani yana Dan shekara goma.

Ba wai su kadai bane a cikin magabata Amma saboda takaitawa.

Mu Hadu a kashi na 004 insha Allah.

           Fassar wasiyyoyi
     Abdurrahman Adamu Aliyu Jahun
   

No comments