WASIYYOYI GA MAHADDATA QUR'ANI 002

Share:
WASIYYOYI GA MAHADDATA QUR'ANI 002
      Sako Daga
     Sheikh Mustapha Baba Ilelah
Chairman Bauchi Qur'anic Recitation competition

  1-Menene Haddah?
   2-Wayene mahaddaci?
   3-Hukuncin Haddar Qur'ani

  1-Menene Haddah?
   2-Wayene mahaddaci?
   3-Hukuncin Haddar Qur'ani.

1- MENENE HADDAH
قال الفيروزأبادي في قاموس المحيط:-(ح ف ظ)حفظه،كعلمه:حرسه،وحفظ القران:استظهره وحفظ المال:رعاه فهو حفيظ وحافظ،من حافظ وحفظه.
Wannan kamar yadda kalmar Haddah tazo Kenan a wajen maluman yaren larabci.

WAYENE MAHADDACIN QUR'ANI
- Malamai su kace in an ce Haddah to Ana nufin barin mantuwa kamar ace:-wani ya karanta Qur'ani akan halcensa,A cikin zuciyar sa watoya haddace.
- Malamai su kace akwai banbancin mahaddacin Hadisai,wakoki,da mahaddacin

 Qur'ani saboda abubuwa guda biyu kamar haka:-
1-Mahaddacin Qur'ani shine wanda ya kammalahaddace littafin gaba da ya,shi ya sa ba'a kiran wanda ya haddace wasu izu kamar 10,20,30,40,50 mshaddacin Qur'ani sai wanda ya haddace izu sittin 60 gaba daya.
2- Dimantar karanta Qur'anin da maimaita shi kullum,shi ya sa wanda ya haddace Qur'ani sai ya bari Qur'anin ta watse a tare dashi ko saboda girma wato tsufa,ko ciwo,ko wata dalili ba'a kiransa mahaddacin Qur'ani.

HUKUNCIN HADDACE QUR'ANI
قال الإمام الزركشي في كتابه البرهان في علوم القرآن(1/457)
Haddar Qur'ani farilla ce da wani ke dauke ma wani,saboda haka wajibi ne Haddar Qur 'ani akan al'umma.
قال الإمام النووي في المجموع(1/51-52)
Farillar da wani ke dauke ma wani shine kamar abin da babu makawa ga mutane wajen tsaida addininsu da ilimukan shari'ar musulunci,kamar haddace Qur'ani,Hadisai da sauransu.
Kuma duk wanda ya tsaya akan farillar da wani ke dauke ma wani abubuwa ne dake tabbatar da farillar da zamto farillar dole,saboda ya dauke nauyi akan al'umma.

Mu Hadu a kashi na 003 (Falalar Haddar Qur'ani)

           Fassar wasiyyoyi
     Abdurrahman Adamu Aliyu Jahun
   

No comments