HUKUNCIN ASKE WANI SASHIN GASHIN KAI ABAR WANI SASHIN.

Share:
HUKUNCIN ASKE WANI SASHIN GASHIN KAI ABAR WANI SASHIN.


An karbo hadisi daga sahabi Abdullah bin Umar yana cewa Manzon Allah (SAW) ya hana Alqaza'u.
(Bukhari)
"Alqaza'u shine aske wani bangaren gashin kai abar wani bangare. Irin wannan askin makaruhine (Abin k'i) sabida Manzon Allah yaga wani yaro yayi irin wannan askin sai ya umarceshi da imma ya aske duka ko Kuma ya barsa duka. Amma idan ya kasance anyi askin ne dan koyi da kafirai to wannan haramunne saboda koyi da kafirai haramunne.
Allah yasa mudace Amin.

No comments