HUKUNCIN LIMANCIN KURMA A MUSULUNCI !!!

Share:
LIMANCIN KURMA!!!
Tambaya
Assalamu alaikum, malam menene hukuncin bin kurma wanda ba ya ji sallah?
Amsa
Wa'alaikum assalam To dan'uwa limancin kurma bai inganta ba, harma wasu malaman sun hakaito ijma'i akan haka, saboda kurma ba zai iya tsayar da wasu daga cikin rukunan sallah ba, kamar kabbarar harama da karatun fatiha da sallama, don haka binsa sallah zai jawo sallar wadanda suke binsa ta zama ba ta cika ba.
Saidai wasu malaman sun tafi akan cewa, ya halatta ya yiwa kurame irinsa limanci.
Don neman Karin bayani duba: Sharhul-kabir na Abdurrahman dan khudaamah 2\38.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr. Jamilu Zarewa

1 comment: