FALALAR AZUMIN ASHURA DA TASU'A

Share:

FALALAR AZUMIN ASHURA DA TASU'A

عن أبي قتادة رضي الله عنه قال سأل رسول الله صلى الله عليه وسلم عن صوم عاشوراء فقال يكفر السنة الماضية

An Karbo daga abu qatada Al-ansariy Allah ya yarda dashi yace: an tambayi manzon Allah sallallahu alaihi wasallam akan azumin Ashura sai yace: "yana kankare zunubin shekarar data gabata". Muslim ya  ruwaito shi.

عن عبد الله بن عباس- رضي الله عنهما- يقول حين صام رسول الله صلى الله عليه وسلم يوم عاشوراء وأمر بصيامه قالوا يا رسول الله إنه يوم تعظمه اليهود والنصارى. فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: ((فإذا كان العام المقبل- إن شاء الله- صمنا اليوم التاسع)). قال فلم يأت العام المقبل حتى توفي رسول الله صلى الله عليه وسلم.
An karbo Daga abdullahi dan Abbas Allah ya yarda dasu yana cewa: a lokacin da Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam yayi azumin Ranar Ashura kuma yayi umarnin azumtarsa sai sukace ya Manzon Allah! Lallai rana ce da yahudawa da nasara suke girmamawa, sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam yace: "To idan shekara mai zuwa ta zo In Allah ya so, zamu azumci Ranar tara" yace: to shekara mai zuwa bata zo ba har sai da Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yayi wafati.
Muslim ya ruwaito shi.

No comments