[ Fatawa] ZAN IYA YIWA MAMACI LAYYA ?

Share:
ZAN IYA YIWA MAMACI LAYYA ?
Tambaya
Assalamun alaikum, malam ko ya halatta na yiwa Mahaifina Layya bayan ya mutu don kawai na kyautata masa?
Amsa
Wa alaikumus salam
Ya halatta ka yi masa, saboda sadaka ce,  sadaka kuma ta halatta ga mamaci, zai kuma iya samun ladanta, saboda hadisai sun tabbatar da cewa mamaci yana iya amfana da sadakar rayayye ya masa.
Amma ba'a son dawwama akan hakan, saboda bai inganta Annabi (SAW) ya yiwa wani matacce shi kadai Layya ba, ya kasance yana mutukar son Hamza baffansa, amma bayan an kashe shi, bai taba yi masa Layya ba, saidai yakan yi Layya ga Ahalin gidansa da wanda bai yi layya ba daga cikin Al'umarsa.
Don neman karin bayani duba Bada'i'ussana'iu 5/72 da kuma madalibu ulinnuhaa 2/472
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

No comments