AZUMIN ARAFAT RAN ASABAR INA MAFITA??

Share:
MAFITA??
Sheikh Nasirudden Albany cikin malamannmu na zamani ya kafa dalili da Hadisin Ahmad, Abu Dawuda, Tirmizy da Nasa'i daga Abudullahi bn Busr yace: Annabi s.a.w .yace:
« ﻻ ﺗَﺼُﻮﻣُﻮﺍ ﻳَﻮْﻡ ﺍﻟﺴَّﺒْﺖ ﺇﻻ ﻓﻴﻤﺎ ﺍﻓﺘُﺮِﺽَ ﻋﻠﻴﻜﻢ »
"kar kuyi Azumi ranar Asabar sai dai in na farilla ne"
Yace yana gwada haramcin azumin kowace Asabar in dai ba azumin farilla ne ba.
Duk da girman Malam Albany, Malamai 'yanuwansa ba su amincewa da fatawarsa ba, sannan suka ambato dimbin malamai da suka saba masa kan wannan fahimtar.
Wassu suka ce hadisin an shafeshi ya daina aiki, wannan shine zancen abu dawuda bayan ya rawaici hadisin a littafinsa, Imam Malik yace hadisin na karya ne, Haka dai wassu suka raunana shi.
Amma gaskiyar zance hadisin ya inganta amma ba ya gwada haramcin yin azumin Arafat da makamantanta ko da ya dace da ranar Asabar, saboda dalilai kamar Haka;
(1) Imamul Bukhari ya rawaito cewa Annabi yace:
" ﻻ ﻳَﺼُﻮﻣَﻦَّ ﺃَﺣَﺪُﻛُﻢْ ﻳَﻮْﻡَ ﺍﻟﺠُﻤُﻌَﺔِ، ﺇﻻ ﻳَﻮْﻣﺎً ﻗَﺒْﻠَﻪُ ﺃَﻭْ ﺑَﻌْﺪَﻩُ »
"Kar dayanku yayi azumi ran Juma'a sai in ya azumci ranar da take gabaninta(Alhamis) ko ranar da ke bayanta(Asabat).
(2) Bukhary da Musulim sun rawaito cewa Annabi s.a.w yace:
« ﺃﻓﻀﻞ ﺍﻟﺼﻴﺎﻡ ﻋِﻨْﺪَ ﺍﻟﻠﻪ ﺻَﻮْﻡُ ﺩﺍﻭُﺩَ - ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ - ﻛﺎﻥ ﻳﺼﻮﻡ ﻳﻮﻣًﺎ، ﻭﻳُﻔْﻄِﺮُ ﻳﻮﻣًﺎ ».
"Mafificin Azumi shine irin na Annabi Dawuda, Yayi azumi yau yasha ruwa gobe"
(3) Annabi yana umarni da azumtar kwanakin da suka fi haske a kowane wata 13,14,15, Hakan kan iya fadowa ran Asabar wata rana, amma Annabi bai togace ban da ita ba.
Mafi yawan Malaman da can da na yanzu suna ganin wannan hanin abinda Annabi ke nufi shi shine kadaita azumin Asabar don gudun kar ayi kamanceceniya da Yahudawa masu girmama Asabar, Kamar yanda bai shafi azumin da zuwansa yake yana caccanza rana kamar Ashura da azumin Arfa. Sukace manzon Allah ya kwadaitar a kansu amma bai togace in sun fado Asabarkar ayi ba!
Malamai da su ke fashin baki akan maganganun Manzon Allah sunce wannan bai shafi kebantattun azumi ba kamar Arfa da sauransu.
Duba littafai kamar haka: Almugnyna Ibnu Qudamah, Almajmu'u na Nawawy, Al'insaf, Fatawal Kubra Ibnu Taimiyya, Ibnu Qayyim, Uthaimeen dss.
Malaman Hadisi da suka ambato hadisin da ya hana azumin ranar Asabar ba su fahimcin hanin azumin Asabar hani ne na gaba daya ba.
Abu Dawuda yayi masa taken
ﺑﺎﺏ ﺍﻟﻨَّﻬْﻰِ ﺃَﻥْ ﻳُﺨَﺺَّ ﻳَﻮْﻡُ ﺍﻟﺴَّﺒْﺖِ ﺑِﺼَﻮْﻡٍ
Babi hani kan kebance ranar Asabar da azumi.
Imamul Baihaqy ya masa taken:
ﺍﻟﻨﻬﻲ ﻋﻦ ﺗﺨﺼﻴﺺ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺴﺒﺖ ﺑﺎﻟﺼﻮﻡ
Babin hani kan kebance Asabar da azumi.
Ibnu Khuzaimah yace bayan ya kawo hadisin " ﻭﺃﺣﺴﺐ ﺃﻥ ﺍﻟﻨﻬﻲ ﻋﻦ ﺻﻴﺎﻣﻪ ﺇﺫ ﺍﻟﻴﻬﻮﺩ ﺗُﻌَﻈِّﻤُﻪُ، ﻭﻗﺪ ﺍﺗﺨﺬﺗﻪ
ﻋﻴﺪًﺍ ﺑﺪﻝ ﺍﻟﺠﻢ ".
" ina tsammaninan hana yin azumin ne don yahudawa suna girmama wannan ranar har sun maida itaranar biki"
Kammalawa: Azumutar ranar in ta dace da ranar Arfa ga wadanda basu je aikin Hajji ba Sunnah ne ba haramun ba ne!!
Rubutawa
Ashsheik Ibrahim Muhammad Disina

No comments