IDAN ARNE YA YI YANKA MUSULMI ZAI IYA CI?

Share:
Assalamu alaikum warahamatullah


Tambaya

Assalamu alaikum malam Mutum ne yana tafiya a mota sai ya kade akuya akan hanya kuma taji ciwo sosai sai wani ba musulmi ba ya yanka ta to shin musulmi zai Iya cin naman akuyar tunda tasa ce.?


Amsa

Wa'alaykumussalam
Shari'a ta hallatta cin abincin ahlul-kitabi (yahudu/nasara) don fadar Allah acikin suratul ma'idah aya ta 5.
Malamai suka ce abinci a wannan ayar ya hada da cin naman su..
Sai dai akwai wasu sharudda tattare da cin yankan su kamar haka:

1. Ya zamanto an yanka dabbar ce kamar yadda ake yanka a shari'a wato an yanka ta makogwaro kuma jini ya zuba..da zasu caka mata wuka, ko su shakure ta, ko sa mata shokin har ta mutu to baza'a ciba.

2. Ya zamanto ba sunan wanin Allah aka ambata ba misali suce (da sunan almasifu ko da sunan yesu etc) don fadar Allah suratul baqara 173 da an'aam 121.

3. Ya zamanto abin da aka yanka na daga cikin dabbobin da akeci a shari'a

4. Ya zamanto yankan ba don murnar bukukuwan su na adini ba ne. Aduba littafin Iqtidaa'us-siradil mustaqeem 1/251.

Idan wadan nan sharuddan sun cika to koda ba'a ambaci sunan Allah ba za'a ci.
Shi mai cin sai ya ambaci sunan Allah, kamar yadda hakan yazo cikin hadisin Aisha wanda ke cikin Bukhari 2057.

Wallahu a'alam

MALAM NURUDDEEN MUHAMMAD (MUJAHEED)

No comments