[Fatawa] HUKUNCIN KASHE KWADI

Share:

Duba kaga yadda yakamata kayi da riba daka amsaDuba kaga yadda yakamata kayi da riba daka amsa

                           ﷽

Assalamu alaikum warahamatullah.

 

Tambaya

Assalamu alaikum Malam menene ingancin hadisin da yake cewa: "Annabi SAW ya hana kashe Kwadi saboda kukansu Tasbihi ne ga Allah"?

Amsa

Wa'alaikum assalam, Tabbas ya tabbata a hadisin Abu-dawud mai lambata: (5269) da kuma Nas'i (2/202) cewa: wani likita ya tambayi Manzon Allah akan kashe kwadi saboda sanyawa a magani sai Annabi ya hana shi kashe su.

Duba kaga yadda yakamata kayi da riba daka amsa

Baihaki ya rawaito daga maganar Abdullahi Bn Amri bn Al-Ass cewa "Kada Ku kashe kwadi saboda kukansu tasbihi ne ga Ubangijinsu". Duk da cewa hadisin zai iya daukar cewa ya ji ne daga Manzon Allah saidai Hafiz Bn Hajar yana cewa " Abdullahi bn Amr bn Ass ya shahara da yin riwaya daga malaman Yahudu da Nasara don haka ba dole ne ya zama daga Annabi SAW ya ji ba.

Kashe kwadi haramun ne saboda hadisin Abu-dawud da Nasa'i da ya gabata.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

No comments