RAMADAN ١/٩/١٤٤٠ - 6/5/2019

Share:

Anga jinjirin Watan Ramadan a Naijeriya

Mai alfarma sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar III, wanda shi ne shugaban majalisar koli kan harkokin addinin musulunci a Naijeriya, ya bayyana ganin jinjirin watan Ramadan a garuruwa daban-daban a Najeriya a wani taron manema labarai da aka gudanar a daren Lahadin nan

Dan haka gobe litinin za'a tashi da azumi a kasar Naijeriya.

Sarkin ya yi kira da a yawaita ibada a cikin watan na Ramadan kuma a ci gaba da addu'a ga shugabanni.

Baya ga Najeriya Musulmai a wasu kasashen duniya irin su Saudiyya za su fara azumin na watan Ramadana a gobe Litinin. Ramadan dai wata ne mai alfarma ga musulmi inda ake matsa kaimi kan ibada da addu'o'i.


No comments