[Fatawa] ZAN IYA YIN RAMAKON RAMDANA A RANAKUN LITININ DA ALHAMIS ?

Share:

                             ﷽


Assalamu alaikum warahamatullah


Tambaya:

Assalmu alaikum malam tambayana shine ina rama azumina a litinin da alhms yayi? Ammafa nayi sittu?

Amsa:

Wa alaikum as salam,an yı sabani game da yın sittu shawwal kafin a gama ramuwar Ramadan, zance mafi inganci shi ne : ba za'a yi ba, saboda Annabi (s.a.w)a hadisin Müslim ya sanya ladan sittu shawwal ne bayan kammala Ramadan.

Za ki iya rama azumin Ramdhana ranar litinin da alhamis, saidai ba za ki samu ladan su gaba daya ba, saboda manufar su ta banbanta, saboda ko da ace ibadoji Iri daya ne, in manufar şu ta banbanta kowacce za ta ci gashin kanta, wata ba za ta wakilci 'yar'uwarta ba.

Allah ne mafi Sani.

Dr Jamilu Zarewa.

No comments