[Fatawa] MEYA SA ALJANU SUKE SHIGA JIKIN MUTANE?

Share:

                           ﷽


Assalamu alaikum warahamatullah

Tambaya:

Malam, me yake kawo aljanu jikin Dan adam, Kuma meza a yi a rabu da su?

Amsa:

Wa alaikum assalam,sakaci da ibada da zikirori na daga cikin abubuwan da suke kawo aljanu,duk mutumin da yake yawan azkar yake kuma kiyaye dokokin Allah,da wuya aljani ya shiga jikinsa, Saboda şu zikirorin safe da yamma da na kwanciya bacci da shiga bandaki da fitowa suna kariya daga shaidanu.

Saidai ko da mutum yana da nagarta, aljani yana iya shiga jikin mutum ta hanyar sihiri ko kambun baka, ko yawan fushi.

Ayoyin Alqur'ani na korar aljani daga jikin dan'adam,musamman Suratul Bakara da Kula'uzai biyu da ayatul kursiyyu da surorin tauhidi guda biyu.

Allah ne mafi sani.

Dr jamilu Zarewa.


No comments