[Fatawa] MACE ZA TA IYA DAGA MURYARTA DA KARATUN SALLAH ?

Share:

                      

                        ﷽Assalamu alaikum warahamatullah.


Tambaya :

Malam barka da yau, tambaya zan yi malam. Shin ya halatta mace ta daga murya a cikin karatun sallah kuwa?

Amsa :

To dan'uwa ya halatta a gare ta ta daga muryarta yayin karatun alqur'ani a sallah, sai in akwai wanda ba muharrami ba a kusa, to sai ta yi kasa da muryarta, don kar ya fitinu.

Wasu malaman sun haramta

 shiga ka karanta yadda Aljannu ke shigar mutane                         

 bayyana karatu, in ta ji tsoran fitina, saboda Annabi s.a.w. ya umarci mata da yin tafi a sallah, lokacin da liman ya yi rafkannuwa, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta :1145, sai suka fahimci cewa: Annabi ya umarce su, su yi tafi ne, don kar wadanda ba muharramai ba, su ji sautinta.

Mace tana daukar hukuncin namiji a cikin dukkan hukunce-hukuncen shari'a, in har ba'a samu nassin da ya kebance ta ba, wannan ya sa za ta bayyana karatu a wuraren da yake bayyanawa, in ba'a ji tsoron fitina ba .

Allah ne mafi sani .

Jamilu Zarewa

No comments