[Fatawa] INA FAMA DA CIWON KODA, ZAN IYA CIYARWA A MAIMAKON AZUMI?

Share:

                          ﷽


Assalamu alaikum warahamatullah Tambaya:

Asalamu Alaikum malam inada tambaya, macece bata da lafiya tana fama da ciwon koda, yafara zama mai tsanani sai tasami likitoci suka bata shawara duk bayan minti Talatin taci wani Abu daga Abinci kartakoshi to malam yaya za'a billowa maganar Azumi ciyarwa za'a cigaba da yi ko jira za'a yi sai ta warke ta rama ?

 Amsa:

Wa'alaikum assalam, in har tana tunanin samun sauki kafin wani azumin ya zo, ba za ta ciyar ba, za ta bari ta rama bayan ta samu dama, saboda aya ta: 184 a suratul Bakara ta nuna cewa: wajibin mara lafiya shi ne rama azumin da bai yi ba na Ramadhana bayan ya samu dama a wasu kwanakin.

Mutukar likitoci sun tabbatar ba za ta samu saukin da za ta rama azumi daga baya ba, ya halatta ta ciyar a maimakon kowacce rana.


Allah ne mafi sani.


Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

No comments