[Fatawa] HUKUNCIN WANDA YA CI ABINCI KO ABIN SHA DA RASHIN SANIN CEWA AL-FIJIR YA FITO

Share:

                          ﷽


Assalamu alaikum warahamatullah


TAMBAYA

Nine zanyi azumi saina makara na tashi ankira assalatu Amma ba'a shiga sallah a anguwanmu ba Kuma banji Ana sallah a wani waje ba

Sainace bari nasha ko ruwane

Inasha kawai sainaji an tada kabbara

Shin zanci gaba da azuminne ko Babu azumin


AMSA


Wa'alaikumussalam Warahmatullahi Wabarakatuh, 

Mallamai sun yi sabani game da wanda yaci wani abu ko ya sha akan rashin sanin cewa alfijir  ya riga ya fito zuwa maganganu guda biyu:

(1) kashin farko na mallamai suna ganin wanda ya ci wani abu ko yasha a tsammanin shi alfijir bai fito ba sai daga baya  yasan cewa alfijir ya riga ya fito  to zai cigaba da azumin shi sannan zai rama wannan yinin. wannan shine ra'ayin Imamu Abi haneefa da Malik bin Anas da Imamushshafi'i da Imamu Ahmad bin Hanbal. 

(2) Kashi na biyu na mallamai suna ganin zai cigaba da azumin shi sanna azumin yayi ba zai rama ba. Wannan shine ra'ayin Ishaq bin Rahawaihi da  riwaya daga Imamu Ahmad bin Hanbal   da Imamul Muzani da  Ibnu Taimiyya da  Dawuduzzahiri  da Ibnu Hazmi, dawasu daga cikin magabata, dalilansu fadin Allah (S.W.T): ربنا لا تؤاخذنا إن نسينا أو أخطأنا'

Ya Allah kada Ka kama mu da laifin da mukayi akan mantuwa ko kuskure, Suratul baqara, Aya (286).

Shiyasa sukace wannan shi kuma yayi ne akan rashin sani kuma duk wanda yayi abu akan rashin sani ba'akamashi da laifi.

Sannan suka kara kafa hujja da fadin Allah SWT 'وليس عليكم جناح فيما أخطأتم به ولكن ما تعمدت قلوبكم'

Babu laifi akan abin da kuka yi shi akan kuskure matukan bakuyishi da gangan ba.

Sai kuma suka kafa hujja da hadisin Asma'u bintu Abibakar wanda tayi tafiya da Annabi (s.a.w) sai suka yi buda baki akan kuskure sai daga baya suka gane cewa rana bata fadi ba, Imamul Bukhari a cikin littafin shi Aljaami'ussahih hadisi da (1959).

Amma Abinda Mallamai suka rinjayar ra'ayi na biyu cewa azumin shi ya yi bazai rama ba.

                  والله تعالى أعلم

No comments