[Fatawa] DALIBIN DA YA YI AURE DA NIYYAR SAKI, IN YA GAMA KARATUNSA ?

Share:

DALIBIN DA YA YI AURE DA NIYYAR ŞAKI, IN YA GAMA KARATUNSA ?

Tambaya:

Malam shin ya halasta mutum ya je karatu wata kasar da Ba nasa ba zai yi shekara 5 sai yayi aure da niyan idan ya gama makarantan nashi sai ya sake ta, ya koma gida?

Amsa:

Wa alaikum assalam,wasu malaman sun halatta hakan,sai dai zance mafi inganci shi ne rashin halarcinsa,saboda ya yı kama da auran mutu'a, sannan kuma hakan ya sabawa wasu daga cikin manufofin aure, Kamar dawwamammar soyayya da kuma debe kewa,

 http://www.abuabdullah.com.ng/2019/05/fatawa-mace-za-ta-iya-daga-muryarta-da.html da cewa: 

Aya ta 21 a suratu Arrum ta  shar'anta aure ne don ka nutsu da matar da zaka aura, wannan manufar ta goce a aure da niyyar saki.

Allah ne mafi sani

Dr Jamilu Zarewa

No comments