SHIN YA HALATTA NA AURI WANDA BA AHALUSSUNNA BA

Share:

Assalamu alaikum warahamatullah.

                        ﷽                       Tambaya:

Slm Malam ya halalta mace ta Auri wanda ba dan Ahlul sunnah ba?????? Don Allah ina son aba mu Hujjoji saboda ta samu abinda zata kare kan ta da shi.                           Amsa

To 'yar'uwa Annabi ﷺ yana cewa: "Idan wanda kuka yarda da addininsa da dabi'unsa ya zo muku, to ku aura masa" kamar yadda Tirmizi ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 1084.


Malamai suna cewa wannan hadisin yana nuni akan cewa duk wanda ba'a yarda da addininsa ba, ba za'a aurar masa ba, wannan sai ya nuna cewa duk wanda bidi'arsa take kaiwa zuwa kafirci, bai halatta a aura masa 'ya ba, don haka duk dan shi'an da yake zagin sahabbai ko yake kafirta su bai halatta a aura masa 'ya ba, saboda ba musulmi ba ne, domin ya karyata Allan da ya yarda da su, haka sufin da yake allantar da shehunansa, ko yake ganin sun fi annabawa, kuma yana sane yake hakan, ba jahili ba ne ko kuma wanda yake da shubuhar da za'a iya warware masa.


Amma duk mai aikata bidiar da ba za ta kai zuwa kafirci ba, to ya hallata a aura masa 'ya, kamar wanda yake yin maulidi saboda son Annabi ﷺ. 


Allah ne mafi saniAmsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

No comments