SHIN WANE SAHABI NE JIKAN SAHABI, BABAN SAHABI

Share:

Assalamu alaikum warahamatullah


                           ﷽    TAMBAYA:

Aslm, don Allah akwai sahabin da kakansa sahabi ne, babansa sahabi, dansa kuma sahabi?, ina son karin bayani malam?

AMSA:

To malam sahabin da yake kakansa sahabi, dansa sahabi, babansa sahabi, shi ne: Abdurrahman dan Abi-bakr bn Abi Khuhafah kamar yadda Ibnu Salah da Ibnul-jauzy suka ambata. Saboda mahaifinsa Abubakar sahabi ne, hakanan kakansa Abu khuhafah shi ma sahabi ne sannan dansa Muhammad sahabi ne, Ibnu Hajar yana cewa: Ba mu san mutum hudu da 'ya'yansu wadanda suka ga Annabi ﷺ ba sai wadannan.


Abin da yake nufi shi ne: Muhammad da mahaifinsa Abdurrahman da kakansa Abubakar da kakansa na biyu Abu-kuhafah dukkansu sun ga Annabi ﷺ don haka su kadai suka samu wannan darajar, Allah ya kara musu yarda.


Don neman karin bayani duba tarjamar Muhammad a Usudul-gabah a lamba ta: 6083.


Allah ne mafi sani.


Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

No comments