[Fatawa] Wanda yayi mantuwa bai yi sudda ba'adi ko qabli bayan

Share:


                         ﷽

TAMBAYA:

Assalamu alaikum

Tambayata itace shin menene hukuncin wanda yamance sajadar kabli ko ba'adi yayin da ta kama shi?.```

AMSA:

ﻭﻋﻠﻴﻜﻢ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ .

ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ ،

Imam Mardaawi (Rahimahullah) yace acikin Al-musannaf (2/154) na Ibn Qudamah: A rankon sajadar mantuwa Akwai sharadi guda biyu.

1.Ya kasance cikin masallaci.

2. Ya kasance aikin baiyi tsawo ba. Ma'ana ba'a samu tazarar lokacin yin mantuwar da tinawa ba.

Wannan shine ra'ayi mai kyau kamar yadda Al-Mardaawi yace.

Imam Ahmad (rahimahullah) yace; Zaiyi sajadar ne idan ya tina anan kusa. Koda kuwa ya fita daga masallacin ne.

Kuma yace zaiyi sajadar koda bayan lokaci mai tsawo ne ya tina, ko kuma yayi magana, ko kuma har bayan ya fita masallaci ne. Wannan shine ra'ayin da Shaykhul Islam Ibn Taymiyyah ya zaba.

Al-Ikhtiyaaraat al-Fiqhiyyah, Shafi na 94).

Idan mutum ya manta sujudar mantuwa wacce zaiyi kafin sallama (Sajadar Qabli kenan), har ya sallame bai tina ba, toh zaiyi sujudar qablin ne anan take kuma wajibi ne yinta (idan ya tina anan kusa).

Amma idan kuma ya sallame kuma Bai tina ba har sai bayan an dauki lokaci mai tsawo, ko ya fita daga masallaci, ko alwalarsa ta warware. Toh anan babu bukatar yin sajadar mantuwa, kuma sallasa ta inganta.

Al-Rawd al-Murabba’ Sharh Zaadal Mustaqna’ (2/461)

MISALI:

Idan mutum ya manta tahiyar farko, anan sajadar qabli ta kamashi, toh sai ya manta ya sallame batareda yayi qabli ba, toh zaiyi qablin ne idan ya tina nan take.

Amma idan bai tina ba anan kusa har sai bayan wani lokaci mai tsawo ko ya fita masallaci, toh anan bazai yi sajadar qablin ba kuma sallarsa tayi.

Shaykhul Islam Ibn Taymiyyah yace zaiyi sajadar ne idan ya tina, koda ya tina ne bayan lokacin mai tsawo. Saboda hakan zai zama cikon abinda ya bari ne a sallarsa.

Amma Ra'ayin da yafi kyau shine ra'ayin Mawallafin (rahimahullah) Wanda shine idan bai tina ba sai bayan lokaci mai tsawo, toh bazai rama sajadar ba kuma sallarsa tayi. Idan kuma ya tina anan kusa zaiyi sajadar.

No comments