[Fatawa] YAYA AKE ZAKKAR KIFI DA KAJI ?

Share:

Assalamu alaikum warahamatullah.


                           ﷽

TAMBAYA:

Asalamu Alaikum Malam ya ka ji da jama'a, tambaya, ta ita ce idan mutum yana kiwon Kifi ko kaji in ya tashi sayarwa sai ya fitar musu da Zakka?.

AMSA:

Wa alaikum assalam, kifi da kaji ba sa cikin abubuwan da ake fitar musu da zakka, amma idan kudin da kika sayar sun Kai nisabi, to in kin ajjiye sun shekara za ki fitar musu da Zakka.

Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Zarewa.


No comments