[Fatawa] WAJABCIN SAMAR DA WURIN ZAMA GA MATAR DA AKA SAKA

Share:

                             ﷽Assalamu alaikum warahamatullah.TAMBAYA

Assalamualaikumm

 Malam shin ya halasta mijjin da yasaki matarsa mai shayarwa ya sama mata wajen zama harta yaye yaron. Nagode


AMSA


Wa'alaikumussalam Warahmatullahi Wabarakatu, 

Idan sakin da ya yi mata saki ne na kome to dole ne zai barta ta yi  idda cikin gidan shi kuma zai ciyar da ita  sai dai idan ta aikata alfasha bayyananne, Ibnu Abbas da Ibnu Mas'ud da  Sa'id Ibnul Musayyab  da Hasanul  Basriy da sauransu sunce shine zina, amma wasu mallamai suna ganin idan tana yiwa iyayan shi ko yan uwanshi rashin kunya ko ta yi wani laifi na sabon Allah mai girma yana  halasta ya fidda ita daga gidansa. Shi yasa Allah(SWT) Ya ce: 

 لا تخرجوهن من بيوتهن ولا يخرجن إلا أن يأتين بفاحشة مبينة( سورة الطلاق آية 1)

Amma idan sakin da yayi mata ba na kome ba ne to anan ba dole bane yasama mata wurin zama a gidan shi domin yin idda.   mallamai dayawa suna ganin fita daga gidan shi  yafi  sai takoma  tayi idda a gidansu.

Domin neman karin bayani za'a iya duba  littattafannan :

1-جامع البيان عن تأويل آي القرآن لابن جرير الطبرى، ج٢٣، ص:(٣٥).

٢-الجامع لأحكام القرآن للقرطبي،ج١٨،ص: (١٥٥).

٣-المصباح المنير في تفسير ابن كثير،ص:(١٤١٣).

والله تعالى أعلم

No comments