[Fatawa] HUKUCIN AMFANI DA MAGANIN DA YAKE HANA HAILA

Share:

Assalamu alaikum warahamatullah.                             ﷽


Tambaya


Assalamu alaikum Allah ya gafarta malam, azumi ya zo ni kuma ba na son na sha ko azumi daya, to shi ne na sayi maganin da zai hanani yin al'ada na sha, bayan mun hadu da kawata, sai take ce min wai babu kyau, shi ne na ce mata ban yarda ba, zan tambayi malamai, don Allah malam a kara min haske ?

 

Amsa


Wa alaikumus salam To 'yar'uwa amfani da maganin da yake hana haila ya halatta, amma da sharuda  guda biyu :


1. Idan ya zama ba zai cutar ba, amma idan zai cutar, to ya haramta saboda fadin Allah “kar ku jefa kawunanku a cikin halaka” suratu Albakarah aya ta 195

 

2.Ya zama da iznin miji ne, idan hakan ya shafe shi, kamar idan tana iddar da ciyarwa ta wajaba akanshi,  to anan bai halatta ta yi amfani da abin da zai hana haila ba saida izninsa, haka nan idan ya zama maganin zai hana daukar ciki to a nan ma dole saida iznin miji.

Saidai  duk da cewa hakan ya halatta da sharudan da suka gabata, amma barinsa shi ya fi, sai idan bukatar hakan ta ta so,  saboda mutum ya zauna akan yadda yake ya fi masa kwanciyar hankali akan ya yi  abin da zai canza dabi’arsa, musamman ma wasu daga cikin kwayoyin na zamani suna dagula kwanakin haila, kamar yadda ya bayyana gare mu, sai a kiyaye.


Don neman karin bayani, duba :  Dima'uddabi'iyya shafi na : 54 .


Allah ne mafi sani.


Amsawa


DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

No comments