[Fatawa] BA'A YIN WUTIRI BIYU A DARE DAYA

Share:

                                          ﷽


Assalamu alaikum warahamatullah


Tambaya:

Assalamu alaikum, don Allah Malam amma naji wasu sunce wai idan mutum yayi wuturi a lokacin da yayi sallah tarawi, toh wai idan zaiyi nafila a cikin dare zai kara raka'a daya ya cika wuturin da yayi da sallah tarawi. Shine nake neman karin bayani malam?

Amsa:

Wa'alaikum assalam, Annabi ﷺ yana cewa ba'a wutiri biyu a dare daya, Na'am akwai malaman da suka faɗi siffar da ka ambata, saboda in ka yi hakan zai zamar da waccan ta farkon shafa'i, tun da wutiri daya ake yi a dare kamar yadda Ibnu Rushd y'a ambata a littafinsa na Bidayatul Mujtaheed.

Amma abin da yafi shi ne ko dai barin wutirin tare da liman ko kuma in ka san za ka sake wata sallar daren In liman ya yi sallama kai sai ka tashi ka karo wata raka'ar don ta zama shafa'i kai a wurinka kafin ka yi sallama, wannan zai sanya ya zama ba ka yi wutiri ba a lokacin.

Annabi ﷺ yana cewa: "Ku sanya sallarku ta karshe da daddare ta zama wutiri"

Allah ne mafi sani

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

No comments