[fatawa] AMFANI DA NA'URAR P.O.S LOKACIN CIRAR KUDI?

Share:


Tambaya

Assalamu alaikum, Malam menene hukuncin amfani da na'urar "P. O. S" yayin cirar kudi, Maimakon mutum ya je banki,  sai ya je ya bawa wani lambarsa ta banki, sai ya yi amfani da na'ura ya juya kudin zuwa na shi banki, sai ya ba shi su a hannu tare da amsar lada ?


Amsa


Wa'alaikumus Salam 

To dan'uwa amfani da P. O. S.  zai iya shiga cikin kiyasu-Ashshabah (قياس الشبه) a ilimin Usulul fiqh, saboda idan aka kalli P. O. S. ta wani wajen yayi kama da haramun domin za ka bada dubu goma a baka naira (9,800), saboda a wurare da yawa duk dubu daya suna amsar ladan naira 20 ne, to kaga ta nan wurin zai iya zama haram kasancewar an samu fifiko, a tsakanin kudi da kudi, samun fifiko kuma tsakanin kudi da kudi haramun ne. 


Akwai kuma bangaren da zai iya zama halal idan aka kalli cewa mai cirar kudin an rage masa wani abu na lokacinsa tun da idan banki mutum zai je ya ciri kudin zai hau mota zai bata lokaci, sannan kuma banki duk withdrawing din da za ka yi in dai  conventional bank ne akwai abinda za su cira daga cikin account dinka, ka ga ta nan bangaren zai iya zama halal kasancewar aiki mai P.O.S ya yi aka biya shi.

Akwai fatawar malamai a  Saudiya wadanda suke ganin cewa idan mutum ya ajjiye kudi a banki kuma kudin nasa ba su da yawa, ya halatta  bankin ya dauki wani abu na ladan aikinsa, saboda wahalar da ya yi na kula da kudin,  a bisa wannan fatawa  P.O.S. zai iya zama ya halatta kasancewar mutum aiki ya maka ya kuma rage maka lokaci sannan kuma ya wakilceka a charges din da banki za suyi maka idan za ka ciri kudi daga account dinka.


 Duk mutumin da bai shiga larura ba kar ya yi amfani da P.O.S. saboda ladan da ake amsa ya fi kudin da banki yake caja, sannan nisantar shubuha  ginshike ne a sharia,  amma wanda ya shiga lalura ya halatta  ya yi amfani da shi gwargwadon lalurarsa saboda abin da ya gabata.


Allah ne mafi sani


Dr. Jamilu Zarewa

No comments