[Fatawa] Akan Ragowar yadin da Tela zai aje bayan gama dinki

Share:

TAMBAYA

Assalamu alaikum 


Malam ni TELA ne dazu wani BAWAN Allah yabani wata fatawa ta tsoratani sosaiYace duk Wanda yayi ragowar yadi komi qanqatarshi inbashi abinsa.


To ni yadda nake Idan bashida yawa sai in ajiyeshi idan wani yakawo baikaimasaba sai inqara masa da ragowar NA wani.


Dan Allah menene mafita?


Nagode Allah yasaka da Alkhairi.AMSA


 Tabbas manzon Allah Saw ya hana ka mallakawa kanka ko ka mallakawa wani hakkin da ba naka ba.

  Hadisi ingantacce, Manzon Allah saw yace Ku maidawa masu hakki hakkinsu, kafin ranar da bazaku iya biya ba. Sai wani sahabi yace, KODA WANNAN ABIN DAN KANKANE NE? Sai manzon Allah saw yace, KODA ZAREN ASUWAKI NE. Wato koda irin citon da mai yin Asuwaki yake furzarwa ne daga bakinsa Sai ka biya, indai hakkin wani ne.

  To kaga ina maganar Wanda yaci yadi? Ae hakkin babba ne. Sabida haka, zaka nemi izininsa ya halatta maka ko kuma ka maida masa hakkinsa.


Allah shine masani.

No comments