[ Yanzu ku duba ] Kota ta yanke wani hukunci kan PDP a Kano

Share:
Assalamu alaikum warahamatullah

A yau dai ne wata kotu a kano ta dakatar da dan takar PDP daga takara watau Abba Kabir Yusuf wanda akafi sani da Abba Gida Gida daga takar dayake yi a jam'iyyar PDP bayan zaman koton a yau litinin 4/3/2019 bayan shigar da karar abokin hamayyarsa yayi wannada sukayi zaben fidda gwanin jam'iyyar da zargin anmasa a ringizo da kwacen kujerarsa ta takara.

Alkalin kotun, Lewis Allagoa ya yanke hukuncin cewa jam'iyyar ta PDP ba ta gudanar da zaben cikin gida ba, saboda haka kotun ta rushe zaben.

Dan takarar gwamnan a jam'iyyar ta PDP, Ali Amin-little, ne dai ya shigar da karar yana kalubalantar yadda aka yi zaben da har Abba Kabir Yusuf ya zama dan takara.

Abba Kabir ne dai dan takarar jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, babban mai hamayya da gwamna mai ci kuma dan takarar jam'iyyar APC.

Bayan kotun ta soke takarar Abba, yanzu ta ba jam'iyyar PDP mako biyu da ta gudanar da zaben fitar da dan takara.

Wannan na zuwa ne, yayin da ya rage kwanaki a gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jiha a Najeriya.

Don samun cikon bayanin sai a kasance tare da mu in Allah ya yarda zamu kawo maku

Almustapha suleiman kankia

No comments