Nazarin matashin nan dan gwagwarmaya a yanar gizo dan asalin jahar Kano wato Bashir Sharfadi

Share:

Abinda Yasa Hausawa Basa Cin Ribar InternetBayan dogon nazari da yawan bibiyar Social Networks da kuma Social Media na fahimci abu guda daya wanda shine ya sanya mutanen mu basu fiya cin ribar internet ba.Menene?

Shine mafi yawan Hausawa mun maida hankali wajen yin Downloading wato saukewa/daukowa muke yi, kullum burin mu shine mu hau Network mu karanta abinda wani ya rubuta ko mukalli hoto ko videon da wasu suka dora.

 Haka bangaren Games, Apps, d.s.

Idan an bamu assignment a makaranta sai muje mu nemi wanda wasu suka saka a internet, bama yin kokarin yin namu.

Masu dorawa daga cikin mu 'yan tsirarune da basu taka kara sun karya ba.A Internet Uploading Dorawa/Sanyawa shine yake kawo riba kudi ko Followers Mabiya to mu kunga abinda muka mayar da hankali shine saukewa, shin ta yaya zamu ci ribar shafukan?An Barmu A Baya

Yau duk abinda kayi searching da yaren Nasara to zaka samu amsarsa a Internet, kamar yadda dukkanmu muna amfani da internet din muna gani.Shin Baka so ace yau shima harshen Hausa ya zama haka?

Ko ka san suma turawan ba wani suka dauki nauyi don ya dinga yi musu aikin sakawar ba, a'a kowa yana iya kokarinsa ne har suka kai ga haka.Misali ni na iya dinki sai na dora yadda ake dinki da Hausa kai kuma ka iya hada Jaka, ko Takalmi d.s kai ma sai ka dora, ba wai abinda wane yayi duka shi za muyi ba.Ka san ribar hakan?

Kana sharewa 'yan baya hanya, nan da shekaru masu zuwa mutane da dama zasu amfana da kai, za'a tuna da kai 'Ya'yan da ake haifa yanzu nan gaba zasu zo suna bincike sai suci karo da bayananka.

Idan mutum ya yiwa abinsa tsari kuma zai dinga samun kudin shiga.Basheer Sharfadi

Social Media Strategist

30-11-2018.

Email: info@sharfadi.com

WhatsApp: 09035830253a

No comments