[Fawata] Minene hukuncin Sakin Hannu a Sallah sunnah ne koko?

Share:

                         ﷽ 

Tambaya:

Assalamu alaikum, malam don Allah a warware mana abin da wannan matar take cewa : Ita maganar rike hannu a salla sunna ce ta shugaba saw. haka nan sakin hannu kamar da yake a bukhari da muwadda duk sun nuna cewa Shugaba a farkon rayuwarsa ya saki hannunsa a Sallah, daga baya ya kama hannu daga Karshen Rayuwarsa yaci gaba da sakin hannu, to kunga sunnar da Shugaba yayi sau biyu tafi wadda yayi sau daya.

Imamu Malik Imamu Darul hijra a mazhabarsa rike hannu a Sallar Farilla Makruhi ne kuma shine Malamin sauran malaman mazhabar da suudiyya take bi, don haka sakin hannu bazai zamo bidia ba, kuma ba zamu nunawa imamu Malik sanin Sunnar Annabi saw ba. Ya kamata jamaa musan cewar in mutum bai rushe mana abinda muke kai ba be kamata mu mu rushe masa nasa ba.

*Amsa:*

Wa alaikum assalam To 'yar'uwa rike hannu a sallah sunna ne kamar yadda Wa'il dan Hujr ya rawaito ya ga Annabi S.a.w yana yi a cikin sallah, kamar yadda ya tabbata a SAHIHI Müslim a hadisi mai lamba ta: 401.

Babu ko hadisi guda daya Wanda ya tabbata cewa Annabi s.a.w yana sakin hannu a sallah, ko da a kaddara ya saki a farkon musulunci daga baya ya rike, sakın ba zai zama sunna ba, tun da Annabi s.aw. yana aiki ne da wahayi, wahayi kuma a hankali yake zuwa, kamar yadda ba'a shar'anta sallah ba sai a daren Isra'i, babu kuma wanda zai ce barin sallah ya halatta tün da babu ita a farkon musulunci.

An rawaito riwayoyi daban-daban daga Imamu Mâlik akan rike hannu a sallah, daga ciki akwai riwayar Ibnul-kasim a Mudawwanah waccce take nuna hallacin rike hannu a Nafila da kuma karhancin rikewa a Farilla, akwai kuma riwayar Ashhabu da Muddarif da Abdulmalik da Ibnu Nafi'i daga Imamu Malik wacce take nuna halarcin rikewa a Farilla da nafila, kamar yadda Ibnu Abdul Barr ya ambata a Istizkar 2/291 da kuma kuma mai littafin Albayan wattahsi a l /394.

Imamu Mâlik ya rawaito hadisin rike hannu a sallah a cikin Muwadda, a lamba ta : 290, saidai wasu malaman suna cewa ya karhanta rikewa a cikin sallar farilla ne a riwayar Ibnul-Kasim saboda ya sabawa aikin mutanan Madina.

Duk da kasancewar Imamu Mâlik bajimin malami mai tsoron Allah, saidai a matsayinsa na dan'adam yana iya yın kuskure, sannan wasu hadisan da ayyukan sahabbai suna iya buya gare shi, kamar yadda ya tabbatar da hakan a maganganunsa, wannan yasa lokacin da halifan zamaninsa ya so ya iyakance aikin mutane a hadisan da suka zo a Muwadda, Imamu Malik ya hana shi, ya kafa hujja da cewa: a wajan malaman Madina kawai ya yi karatu, akwai wasu malaman da bai hadu da su ba.

Rike hannu a sallah sunna ce tabbatacciya daga Annabi s.aw. kuma hakan shi ne aikin mafi yawan sahabbai da tabi'ai da manyan malamai, ba za'a barta saboda wani malami ba, tare da cewa : wanda ya saki hannu a sallah, bai yi laifi ba, kuma sallarsa ta yi.

Allah ne mafi sani.

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA


No comments