[Fatawa]MENENE HUKUNCIN SWAP TEST DA AKE YIWA MATA?

Share:


                          ﷽

MENENE HUKUNCIN SWAP TEST DA AKE YIWA MATA?

Assalamu alaikum.

Tambaya: Malam don Allah ina da tambaya, Swap(smear) test da ake ma mata yana karya azumi?

Zata yi wankan tsarki idan a ka yi? Kuma wadanne dokoki za'a kiyaye yayin yinsa?

AMSA: Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Swap test, ina tsammanin kina nufin irin test din nan wanda ake shigar da na'ura agaban mace domin daukar wasu samfurin Gwaje-gwajen da za'ayi domin gano kosanin wata jinyar dake tare da ita..

To wannan ba ya karya azumi. Kuma mace ba zatayi wankan tsarki saboda shi ba. Sai dai idan an samu fitar maniyyi ta dalilinsa.

Amma idan aka shigar da wani magani tanan din, kuma har dandanonsa yakai ga Makoshi to azumi ya karye, Bisa Mazhabin Imamu Malik (rahmatullahi alaihi).

Hukuncinsa ta fuskar halacci, dole ne ya zamanto Mace ce zatayi ma mace. Ba wai Namiji yayi ma mace ba.

Kuma wajibi ne Matar ta zamto Musulma. Sai dai idan babu musulmar, kuma test din ya zama dole ayishi ko kuma shine ka'dai hanyar samun lafiya gareta, to sai a sanya kafirar tayi.

WALLAHU A'ALAM.

Almustapha suleiman kankia

07035674655

1 comment: