[Fatawa] ZAN IYA BI-BIYAR LADANI LOKACIN DA YAKE TADA IKAMA?

Share:
TAMBAYA: Assalamu alaikum, ina fata malam yana lafiya, bayan haka malam don Allah inada tambaya kamar haka..menene hukuncin maimaita ikama awajen mamu ayayin tada sallah???
AMSA:To dan'uwa akwai hadisin da yake nuni da cewa: ana bi-biyar ladani lokacin da yake ikama, saidai hadisin bai inganta ba, wasu malaman hadisin sun raunana shi, don haka ba za'a iya gina hukunci akansa ba. Saidai akwai malamai da yawa da suke ganin za'a bi-biyi mai ikama saboda Annabi ﷺ ya kira tad a sunan kiran sallah a cikin hadisin Bukhari mai lamba ta: 601, don haka za ta dau hukuncinta.
Zance mafi inganci shi ne: ba za'a bi-biyi mai ikama ba, saboda ibada tana bukatar dalili tabbatacce. Kasancewar Annabi ﷺ ya kira Ikama da kiran sallah da suna daya, ba ya nuna hukuncinsu daya ne, saboda idan abubuwa biyu suka hadu ana iya kiransu da sunan daya daga ciki, kamar yadda ake cewa Wata da rana: watanni biyu.
Don neman karın bayani duba: Almajmu'u na Nawawy 4/122 da kuma Likaa'u babi Almaftuh na Ibnu uthaimin: 219.Allah ne mafi saniAmsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Almustapha suleiman kankia

No comments