[Fatawa ] WANDA YA NEMI MATAR DA TAKE IDDA, ZAI IYA AURENTA BAYAN TA KAMMALA.

Share:

                          ﷽

WANDA YA NEMI MATAR DA TAKE IDDA, ZAI IYA AURENTA BAYAN TA KAMMALA

Tambaya: Assalamu alaikum. Allah ya kara ma malm lafiya da tsawan rai mai albarka.

Tambayata shine idan wani ya nemi macen da take idda yace mata yana son ta kasance matar shi nan gaba, wai aure ya haramta a gare su in ta gama iddan?

Amsa: Wa'alaikum assalam, ya aikata sabon Allah, tun da Ubangiji ya haramta neman auran wacce take idda a cikin suratul Bakara aya ta: (235).

Ya halatta a gare shi ya aure ta bayan ta kammala idda, saboda wancan sabon ba zai haramta masa ita ba.

Idan har aka daura aure a cikin idda, malaman Malikiyya suna wajabta raba auran da kuma haramtata ga wanda ya auretan har abada.

 Da fatan kun fahimci bambanci tsakanin neman aure da kuma daura aure a cikin Idda.

Allah shine mafi sani 

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

No comments