[Fatawa] Tambaya ta Hudu 4] Ina hukuncin masu Hakoran Gwal game da wankan Janaba?

Share:
                           ﷽

 Assalamu alaikum warahamatullah.

TAMBAYA: Ina hukuncin masu Hakoran Gwal game da wankan Janaba?

AMSA: To, baki bai cikin zahirin jiki; saboda haka, ba a cewa wankan janabarsa ya baci. Sannan kuma duk abinda yake yana da dan asali ga shari'a, to, kar a matsa wa musulmi ga me da shi. Watau, abinda bai da asali shi ne za a tsananta wa musulmi (a kan shi).

Ya halatta mutum ya daure hakora da zinari, ko ya sa gun kawar Alkur'ani. Saboda haka, idan an ga wani mutum ya yi sai a ce: yana da wani dan sanadi; ba za a damu ba. Kullum ba ayi wa mutum musu, sai ga abin da ba shi da wata hujja, ko 'yar yaya.

ASSHEIAK ABUBAKAR GUMI

Almustapha suleiman kankia

No comments