[Fatawa Tambaya ta Daya 1] utun ne yayi bawali (fitsari); sai bai sami ruwa ba, haka nan bai sami dutse ba; sai ya karkabe. Da kuma lokacin sallah ya yi, sai ya tafi ya yi alwalla ya yi sallah. To ya ya sallarshi?

Share:
                         ﷽

TAMBAYA 1: mutun ne yayi bawali (fitsari); sai bai sami ruwa ba, haka nan bai sami dutse ba; sai ya karkabe. Da kuma lokacin sallah ya yi, sai ya tafi ya yi alwalla ya yi sallah. To ya ya sallarshi?

AMSA: To, in dai ya karkabe, yana da alwalla. Cewa aka  yi "kada ka yi sallah, kana dauke da kazanta". Watau dai, in ya sa hoge,  ko yasa dutse, ya goge, ya je ya yi alwalla ya yi sallah, ya halatta. Amman idan bai yi ba, har ya zan akwai kazantar nan gareshi,  sannan ya yi alwalla; bai tuna ba sai bayan ya gama sallah; in akwai lokacon sake sallar nan (lokacinta bai fita ba) to, sai ya sake. in kuwa babu lokaci, shi ke nan sallar sa tayi. Domin kuma akwai Ruwaya, ga khalifa gun Malik, cewar: shin gusar da kazanta, ga tufar mai sallah,ko jikinsas, ko wajen zamansa; wajibi ne, ko sunnah? In ance wajibi ne,to ko lokaci ya wuce sai an sake. Amman in an ce sunnah ne, to in lokaci ya wuce ba za a sake ba.

To, amman ko a inda Malik ya ce wajibi ne, yasa sharudda biyu: in da yake mutun ya tuna, kuma yana da ikon gusarwa. To, a nan indai bai tuna ba fa? ko bai da ikon gusarwa? To, ashe ke nan sai akwai lokaci 

zai sake.

Sheik Abubakar Mahmud Gumi

(Allah yajiqansa da Rahama)


Almustapha suleiman kankia

No comments