[ Fatawa Tambaya ta Biyu 2] Malam ko ya halatta mutum ya yi sallah da Belt na fata a jikin shi?

Share:

                           ﷽

TAMBATAYA: Malam ko ya halatta mutum ya yi sallah da Belt na fata a jikin shi?

AMSA: Eh, idan fatar Belt din ta fito daga kasar musulmi nest, ko kuma kasar kiristoci, ko kuma kasar yahudawa, yana halatta mutum yayi sallah da Belt din.

Amman  in fatar ta fito daga kasar Arna (masu bin addinin Gargajiya, ko masu Bautar Rana ko Wuta ko Gumaka,da dai sauran irinsu), Wadanda yake ba a cin yankansu, to  bai halatta a yi anfani da irin wannan Belt din ba, a wajen Sallah.

Haka nan in mutum na kokanton ko daga ina fatar Belt din ta fito, shima ba zai yi anfani da ita wajen sallah ba.

Sheik Abubakar Mahmud Gumi

(Allah yayi mashi Rahama)

Almustapha suleiman kankia

No comments