[Fatawa Tamabaya ta ukku 3] Allah ya gafarta Malam, mutum ne ya auri yarinya, sai ya kasance ba ta yin wankan janaba. Me ya kamata ya yi? Kuma idan ta haihu a irin wannan hali, yaya matsayin dan da ta haifa?

Share:

                          ﷽

Assalamu alaikum warahamatullah

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, mutum ne ya auri yarinya, sai ya kasance ba ta yin wankan janaba. Me ya kamata ya yi? Kuma idan ta haihu a irin wannan hali, yaya matsayin dan da ta haifa?

AMSA: To wannan ita fasika ce. Ya kamata ka yi lallashinta, ka nuna mata hikimar da ke ciki. In abu ya buwaya kana iya sakin ta. Amma dai in ba ta karyata cewar wankan janaba ba gaskiya ba ne tana nan musulma ko ba ta yin wankan. Amman in ta karyata wankan janaban, ba ka iya aurenta.

Game da dan aka haifa cikin irin wannan hali kuma, yana nan a danshi, kuma Musulmi. Domin laifin daban hukuncin danta kuma daban.

ASSHEIK ABUBAKAR MAHMUD GUMI


Almustapha suleiman kankia

No comments