[ Fatawa ]SHIN HADISIN SALLAH KARFE TARA (9:00) NA SAFE YA INGANTA?

Share:

SHIN HADISIN SALLAH KARFE TARA (9:00) NA SAFE YA INGANTA?

Tambaya:

Assalamu alaikum, Da farko Allah ya saka ma malam da alkhairi, tambayata a nan ita ce, ya matsayin yin sallar juma'a da karfe 9:00 na safe kuma a wani hadisi aka samo yin haka kuma ingantacce ne ko kuma da''ifi ko maudu'i ne hadisin?. Allah bada ikon amsawa dai dai (amin).

Amsa:

Wa alaikumus salam, wasu malaman sun fahimci halarcin yin sallar juma'a kafin rana ta yi zawali a wani hadisi tabbatacce a sahihul Bukhari, sai dai mafi yawan Malamai ba şa aiki da shi, saboda ba akansa Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya dawwama ba, mafi yawan lokuta Annabi ya na yin sallar Juma'a ne bayan rana ta yi zawali, haka ma halifofinsa shiryayyu.

Duba maslaha yayin aikata hukuncin sharia ginshiki ne mai zaman kansa a sharia, wannan ya sa Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ki sake ginin Ka'aba da mayar da ita yadda take a zamanin Annabi Ibrahim don kar Kuraishawa şu fıtinu, tare da cewa ya so hakan, amma sai ya bar shi saboda maslaha.

Wanda ya yi sallar juma'a kafin rana ta yi zawali sallarsa ta yı, tun da yana da magabata, saidai lura da yanayin mutane yana halatta barin abin da yake ba dole ba, kamar yadda aka rawaito sayyadina Usmanu ya daina Kasaru a hajji saboda wani bakauye ya zamar da sallolinsa na tsawon shekara kasaru duka, bayan ya koma gida, saboda aikin sayyadi Usmanu da ya gani.

Allah Ta'ala ne mafi sani.

Dr Jamilu Zarewa.

23/04/2016

Almustapha Suleiman Kankia

No comments