[Fatawa] MUN GAMA SALLAH, ASHE LIMAN YA MANTA BASHI DA TSARKI ?

Share:                       ﷽

Assalamu alaikum warahamatullah
TAMBAYA : Malam mune mukayi sallah muna karewa liman yace yamanta baida tsarki yayi fitsari baiyi tsarki ba. zamu maida wata sallah ne kota limance kawai babu tunda mu da tsarkinmu ko har tashi tayi daidai?

AMSA: To dan'uwa sallar liman ta baci, kuma dole ya sake, amma ku sallarku ta inganta, a zance mafi inganci, saboda dalilai kamar haka :

1. An rawaito daga Umar- Allah ya yarda da shi cewa : ya taba yiwa mutane limancin sallar asuba, bayan an gama sallah, sai ya ga maniyyin mafarki a jikin tufansa, sai ya sake sallah, amma mamun ba su sake ba.

2. Sayyidina Aliyu yana cewa : "Idan mai janaba ya yiwa mutane limanci, zan umarce shi ya yi wanka, ya sake sallah, amma ba zan ce da mamun su sake ba .

3. Abdullahi dan Umar - Allah ya yarda da shi- ya taba yiwa mutane sallar asuba, sai ya tuna ba shi da alwala, sai ya sake amma mamu bas u sake ba.

Abin da ya gabata aikin sahabbai ne, aikin sahabi hujja ne, in ba'a samu wani sahabin ya saba masa ba.

Don neman Karin bayani duba : Almugni 1\419

Amsawa:- Dr Jamilu Zarewa

Almustapha suleiman kankia

No comments