[Fatawa] MIJINA BA YA SALLAH, KO ZAN IYA NEMAN YA SAKE NI?

Share:


                         ﷽

Assalamu Alaikum warahamatullah.


Tambaya:


Assalamu alaikum malam ya karatu, Allah ya kara basira, malam wata mata ce take son a fada mata hukuncin zama da mijinta da bai damu da sallah ba, ko da kuwa lokacin Ramdahana ne, sannan kuma yana tilasta mata ya sadu da ita a lokacin watan Ramdhana da rana, bayan haka yana saduwa da ita tana jinin haila, kuma ta fada masa haramun ne amma ya ki ya daina, shin malam za ta iya neman saki tun da ba ya bin dokokin Allah ko ta cigaba da zama da shi? , na gode Allah ya karawa malam basira da hazaka.


Amsa:

Wa'alaikum assalam To 'yar'uwa mutukar an yi masa nasiha bai bari ba, to za ki iya neman saki, saboda duk wanda ba ya sallah kafiri ne a zance mafi inganci, kamar yadda Annabi S.A.W ya fada a hadisin da Muslim ya rawaito mai lamba ta: 81.


Ga shi kuma aya: 10 a suratul Mumtahanah ta tabbatar da rashin halaccin musulma ga kafiri, kin ga cigaba da zamanku akwai matsala a addinan ce.


Allah ya hana saduwa da mace mai haila a suratul Bakara aya ta: 222, Saduwa da mace da rana a Ramadhana babban zunubi ne kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba ta: 616 ya tabbatar da hakan.


Saidai zunubin barin sallah shi kadai ya isa ya raba aure, idan har bai sake ki ba, za ki iya kai shi kotu, alkali ya raba ku.


Don neman Karin bayani duba Al-minhajj na Nawawy 2\69.


Allah ne mafi sani.


Dr. Jamilu Zarewa.

No comments