[ Fatawa ] Menene Hukuncin auren Kashe-Wuta a Shari'ance??

Share:

Tambaya: Malam Menene Hukuncin auren Kashe-Wuta a Shari'ance??

AMSA: Wato dai Abinda ake ƙira da suna Auren-Kashe-Wuta shine, Mutum yasaki Matarsa har Saki(3), kuma daga baya sai yaji yanason yadawo da'ita to kuma babu damar yinhakan a Shari'ance, to shine sai Mijin suhaɗa baki da wani abokinsa akan cewa abokin ya aureta daga baya kuma yasake sai takoma gidan tsohon Mijinta, wato dai anufinsu shine kamar sunyiwa Shari'ar Aℓℓαн(ﷻ) wayo kenan, Ko-Shakka-Babu cewa auren Kashe-Wuta haramunne bai halattaba, kamar yadda yazo acikin Hadisi Mαɳzσɳ Aʅʅαԋ(ﷺ) Yana cewa:

"لعن الله المحلل والمحلل له" (رواه أبو داود)

MA'ANA:

Aℓℓαн(ﷻ) Ya tsirewa Mai Halattawa (mai Auren Kashe-Wuta) dakuma wanda za'a Halattawa (tsohon mijin kenan)

Danhaka kenan idan Mutum yasaki Matarsa har Saki (3) to bai Halatta yadawo da'itaba dole sai ta auri wani Mijin kuma ingantaccen aure, kuma bawai ya aureta bane da nufin nangaba yasaketa dan takoma wajen tsohon Mijintaba, Sannan kuma Sharaɗine yakasance Mijinda ta auraɗin yataɓa Jima'i da'ita aƙalla koda sauɗayane, to idan Mijin yarasu kokuma yasaketa dan raɗin kansa, to ya halatta takoma wajen tsohon Mijhnta ya aureta, amma idan yazamana cewa Sabon Mijin da taura baitaɓayin Jima'i da'itaba harsuka rabu dashi, to haryanzu batazama halal ga tsohon Mijintaba dole sai tasake wani auren kenan,

Amma idan yakasance Mijin dayasaki Matar saki uku, dama  sunhaɗa bakine dashi da wani abokinsa dakuma ita Matar akancewa shi abokinnasa ya Aureta inyaso daga baya sai yasaketa tadawo wajen tsohon Mijinta, to ko shakka babu cewa wannan haramunne kuma Kaba'irace daga manyan zunubai, Sannan kuma shi wanda ya auretaɗin danufin haka aurensu da'itaɗin Ɓataccene a Shari'a, idanma yasadu da'ita to Zina kawai sukayi, hakanan kuma koda ya saketa to bai halattaba takoma wajen Mijinta nafarkonba, idankuma hartakoma yasake aurenta to sutabbata cewa zaman Daduro (zina) sukeyi,

Amma idan shi wanda ya auretaɗin babu wani haɗin baki dasukayi da tsohon Mijinnata wataƙilama shi tsohon Mijinnata baisanma cewa wannanɗin zai auretaba, amma shikuma wanda zai auretaɗin dama azuciyarsa yanaso kawai ya aureta dan yasaketa taƙara komawa wajen tsohon Mijinta, to shima aurensa da Matar Ɓataccen aurene sakamakon mummunar niyyarsa kuma shima in yasadu da'ita to zina kawai sukayi, danhaka shima koda yasaketa to baihalatta takoma wajen Mijinta nafarkoba,

Amma idan yakasance ita Matarbdama azuciyarta tanasone ta auri wani danufin cewa idan suntare daga baya zatanemi yasaketa kokuma tayi ta munana masa haryagaji yasaketa, to anan sai Malamai sukayi Saɓani, Mazhabin HANABILA dakuma wasu daga cikin Malamai kamar irin su

Hasanul-Basriy,

Ibrahimun-Nakh'iy,

Shaikhul-Islam Ibn-Taimiyya,

Sukace shima wannan nau'ne na auren Kashe-Wuta, danhaka shima bai halattaba sakamakon mummunar niyyarta, Sannan sukace idan ɗaya daga cikin su ukun (wato mijin ko matar kokuma shi wanda zai aura) yayi nufin ayi auren kuma daga baya asaketa takoma wajen nafarko, sukace duk hukuncinsu ɗayane auren baiyiba,

Saidai Mazhabin MALIKIYYA dakuma wani sashe na HANABILA sukace idan har yasaketa to ya halatta takoma wajen tsohon Mijinta sukace niyyarta na auren Kashe-Wuta batada wani tasirin da zata ɓata aurensu, Saidai wasu daga cikin Ma'abota Ilimi sukace Maganar farko tafi ƙarfi, tunda asali bai halatta takomaba harsai tayi ingantaccen aure, amma yanzu taje tayine da nufin nangaba takashe auren awani lokaci sananne sukace bai halattaba, domin yazama kamar tayi auren Mut'ane kenan, Sannan kuma gashi ta yaudari Mijin, ta cutar dashi, ta munana masa, dankawai yasaketa,

Saidai Mafi yawa daga cikin Malamai sukace idan har Mijinta nabiyun yasaketa to yahalatta takoma wajen Mijinta nafarko, sukace duk wanda igiyar aure ba ahannunsa takeba to niyyarsa ta rabuwa batada wani tasiri, domin bata da'ikon ta'iya sakin kanta dakanta dole sai ansaketa, Saidai abinda tayiwa Mijin na yaudara da munanawa sukace ananne takeda laifi, da kamata yayi ace tayi amfani da hanya maikyau wacce Mijin bazai cutu sosaiba, wato ta lallabashi har ya yarda suyi Khul'i ta mayar masa da Sadaƙinsa, hakan shiyafi dacewa:(وَالـلَّـهُ سُـبْـحَـانَـهُ-وَتـَعَــالـَيٰ أَعْـلَـ)

Almustapha suleiman kankia

07035674655

No comments